Daga Karshe, Babban Dalilin Da Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye Hannun Tinubu Ya Bayyana

Daga Karshe, Babban Dalilin Da Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye Hannun Tinubu Ya Bayyana

  • Muhimmin dalilin da ya sa, Atiku Abubakar, na jam'iyyar PDP ya sha kaye a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023 ya bayyana
  • Wani jigo PDP ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta sha kashi a hannun APC ne saboda gurɓataccen jagorancin kwamitin gudanarwa (NWC)
  • Atiku da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party sun lashi takobin kalubalantar nasarar Bola Tinubu, wanda za'a rantsar ranar 29 ga watan Mayu

Sanata Obinna Ogba na jam'iyyar People Democratic Party (PDP), mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya, ya bayyana babban muhimmin abinda ya haddasa rashin nasarar Atiku Abubakar.

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha kaye hannun Bola Tinubu na APC a zaɓen shugaban kasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Atiku da Tinubu.
Daga Karshe, Babban Dalilin Da Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye Hannun Tinubu Ya Bayyana Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu
Asali: Facebook

Ɗan majalisar dattawan ya ce ba abun mamaki bane don jam'iyyar PDP ta yi rashin nasara a babban zaɓen da aka kammala saboda gurbataccen jagorancin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) karkashin Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Ce Jam'iyyar Ta Cancanci Kayen Da Ta Sha a Zabe, Ya Bayar Da Dalilai

Meyasa Atiku ya sha kashi hannun Tinubu?

Ogba, a mahaifarsa da ke ƙaramar hukumar Ishielu ranar Lahadi 9 ga watan Afrilu, ya shaida wa manema labarai cewa NWC da kanta ta kashe kanta ta hanyar baiwa wanda bai dace ba takarar gwamna a Ebonyi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanatan, wanda ya rasa tikitin takarar gwamna a PDP bayan tafka muhawarar shari'a har zuwa Ƙotun koli, ya ce bai kamata NWC ta dakatar da kowa ba a cikin jam'iyya.

Ya ce:

"Maganar gaskiya ita ce mambobin kwamitin gudanarwa NWC ya kamata a dakatar, farawa daga shugaban jam'iyya na ƙasa. Ciyaman na kasa ga gaza kawo eumfa, gunduma, ƙaramar hukuma da jiharsa."
"Haka lamarin yake ga dukkan waɗanda suka ba da haɗin kai aka miƙa tikitin takara ga 'yan korensu."

Har yanzun PDP na da dama - Ogba

Sanata Ogba ya ƙara da cewa duk da abinda ya faru jam'iyyar PDP na da burbushin dama tun da 'yan Najeriya na kaunarta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Kutsa Kai Cikin Sakatariyar Jam'iyya Ta Ƙasa a Abuja

"Abinda muke buƙata mu samu shugabannin da suka san hannun su saboda ba bu jam'iyyar da ta fi karfin PDP," inji shi.

A.wani labarin kuma Mun Kawo Muku Abu 1 da Ya Taimaki Bola Tinubu Ya Iya Lashe Zaben Shugaban Kasa Inji Farfesa Sagay

Farfesa Sagay, shugaban PACAC, ya bayyana hasashensa kan abinda ya taimaki Tinubu ya samu galaba kan sauran yan takara a babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262