Jam’iyyar da ta Goyi Bayan Tinubu, Ta Kai Shi Kotu a Kan Murde Zabe a Jihohi 11

Jam’iyyar da ta Goyi Bayan Tinubu, Ta Kai Shi Kotu a Kan Murde Zabe a Jihohi 11

  • Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta ce ba Bola Tinubu ne ya lashe zaben shugaban Najeriya ba
  • APP ta dauki hayar Emeka Ozoani SAN, ta shigar da kara a kotun da ke sauraron korafin zaben 2023
  • Kano, Kaduna da Kebbi su na cikin jihohin da Jam’iyyar adawar ta ce an yi amfani da kudi wajen magudi

Abuja - Wata jam’iyyar hamayya mai suna APP ta zargi Asiwaju Bola Tinubu da yin magudi a zaben shugaban kasar Najeriya da aka shirya a bana.

A rahoton da muka samu a Premium Times, zargin murdiya yana cikin jerin korafi biyar da Lauyoyin jam’iyyar APP suka gabatarwa kotun zabe.

APP da ‘dan takaranta watau Nnadi Osita ya samu kuri’u 12, 839 a zaben Fubrairu ta na so kotun sauraron karar zabe ta rusa nasarar da INEC ta ba APC.

Kara karanta wannan

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

Masu shigar da kara sun ce ‘dan takaran na jam’iyyar APC ya yi amfani da kudi wajen saye ma’aikatan zabe a yankunan Kano, Kaduna da Kebbi.

An murde zabe da kudi?

Baya ga jihohin nan, rahoton ya ce jam’iyyar ta yi ikirarin kudi sun yi tasiri wajen nasarar da Tinubu ya samu a Ribas, Oyo, Ogun. Ekiti, Kogi da Kwara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APP ta ce kuri’un da jam’iyyar APC ta samu a jihohin nan har aka ba sauran ‘yan takara tazara ba na gaskiya ba ne, sannan ana zargin APC da sayen kuri’u.

Jam’iyyar APC
'Yan takarar Jam’iyyar APC Hoto: officialasiwajubat
Asali: Twitter

Sauran zargin da ke kan APC

Lauyan da ya tsayawa jam’iyyar hamayyar ya ce an ba masu kada kuri’u kyaututtuka domin su zabi APC, kuma aka hana masu wani ra’ayin kada kuria’arsu.

Har ila yau, APP ta ce akwai garuruwa irinsu Orlu, Orsu da Okigwe da aka gagara yin zabe a Jihar Imo saboda rikici, saboda haka suka tace Tinubu bai ci zabe ba.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Jam'iyyar APC ta kori wani fitaccen sanata a jihar Arewa

Wani korafi da ake da shi a kan zaben shi ne hukumar INEC ta sabawa dokar zabe ta kasa ta 2022 domin ba a daura sakamakon da wuri a kan shafin IRev ba.

Emeka Ozoani SAN ya ce ‘dan takaran APC bai samu 25% na kuri’un da ake nema a Jihohi 24 da Abuja ba. Bayan haka ana zarginsa da karyar shekaru da takardu.

Ina goyon bayan Tinubun?

Abin mamaki, APP ta na cikin jam’iyyu hudu – tare da NRM, ZLP da APM da aka ji shugabanninta na reshen Legas sun marawa Tinubu baya a zaben da ya gabata.

Adeyemi Abiola ya sanar da hakan ana daf da za ayi zaben sabon shugaban Najeriya a Fubrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng