FFK Ga Peter Obi: Ka Mana Alfarma Dan Allah Ka Bar Kasar Nan

FFK Ga Peter Obi: Ka Mana Alfarma Dan Allah Ka Bar Kasar Nan

  • Jigon jam'iyyar APC kuma darakta a kwamitin kamfen Tinubu/Shettima, Femi Fani-Kayode ya maida martani ga Peter Obi
  • Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party ya ce sautin muryan da ake yaɗawa karya ne kuma an matsa masa ya bar Najeriya
  • Feni-Kayode, tsohon minista a Najeriya, ya roki Peter Obi ya taimaka ya tattara kayansa ya fice Najeriya kuma kar ya dawo

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya roki ɗan takarar da ya nemi kujerar shugaban ƙasa karkashin inuwar Labour Party, Peter Obi, ya tattara kayansa ya bar Najeriya kuma kar ya dawo.

FFK da Peter Obi
FFK Ga Peter Obi: Ka Mana Alfarma Dan Allah Ka Bar Kasar Nan Hoto: FFK, Peter Obi
Asali: UGC

Fani-Kayode, Daraktan sashin midiya na kwamitin kamfen shugaban ƙasa a APC, ya faɗi haka ne yayin martani kan kokawar da Obi ya yi cewa yana cikin matsin lamba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Kutsa Kai Cikin Sakatariyar Jam'iyya Ta Ƙasa a Abuja

A ranar Laraba, Peter Obi, ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da kokarin ɗauke hankalin mutane daga kan kura-kuran da ta tafka a babban zaɓen da aka kamma kwanan nan.

Obi ya yi martani kan tattaunawar murya da ta yaɗu tsakaninsa da shugaban Cocin Living Faith Church, David Oyedepo, ya ce an matsa masa ya fice daga Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana kan sautin muryan, wanda 'yan Najeriya suka laƙabawa 'Yes Daddy' tsohon gwamnan Anambra ya ce:

"Abubuwa na ta fitowa suna bayani daban-daban (a kaina), alal misali zargin da Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, ya ɗora mun, sautin murya na tattaunawar waya na ƙarya da aka kirkira, da matsin lambar na bar ƙasa."

Wane martani FFK ya maida wa Peter Obi?

Da yake martani kan kalaman Obi cewa yana cikin matsin lamba ya bar Najeriya a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis, Fani-Kayode ya ce:

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

"Dan Allah ka mana babbar Alfarma ka tafi yanzu, da safe-safe ake kama fara kuma karka dawo har abada."

“Ku Tafi Kotu Sannan Ku Jira Hukunci”: Buhari Ga Atiku

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari Ya Bayyana Abun da Ya Kamata Atiku, Peter Obi da Sauransu Su Yi

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya shawarci waɗanda babban zaɓen 2023 bai gamsar da su ba da su garzata Kotu.

A sakon bikin Easter, shugaban ƙasan ya nemi ɗaukacin 'yan Najeriya da karsu cire rai kuma su riƙa fata mai kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262