Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

  • Biyo bayan sakamakon manyan zabukan 2023, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa lallai mai zabe shine sarki
  • Shugaban na Najeriya ya ambaci yadda wasu gwamnoni suka gaza cin zaben sanata, yana cewa hakan na nufin a yanzu babu wata tabbataciyar hanyar samun mulki
  • Idan za a iya tunawa irinsu Gwamna Okezie Ikpeazu na Abia, Samuel Ortom na jihar Benue sun sha kaye a zaben neman zuwa majalisar dattawa

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis 6 ga watan Afrilu, ya ce kada wani ya sake raina karfin ikon da masu zabe ke da shi a Najeriya.

Shugaban, yayin da ya ke duba zuwa ga sakamakon zabukan 2023, ya tabbatar cewa zamanin samun mulki cikin sauki ya kau.

Buhari.
Buhari ya tarbi sabon Sarkin Dutse, babban birnin jihar Jigawa a fadar gwamnati da ke Abuja. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban na Najeriya ya ce zabukan na 2023 sun nuna wayewa na masu kada kuri'a a Najeriya idan aka zo batun zaben shugabanni, ya kuma ce dimokradiyya a kasar na kara karfi.

Kara karanta wannan

“Kasuwa Bata Yi Mun Dadi Ba”: Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Faduwa Da Ya Yi a Zaben Sanata

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya bayyana abin da ke zuciyarsa yayin da ya karbi bakuncin sabon sarkin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Hamin Nuhu Sunusi, a gidan gwamnati a Abuja.

Ya kara da cewa ya yi mamakin yadda wasu gwamnoni da ke kan mulki suka gaza cin zaben sanata. A cewarsa, hakan na nufin mai kada kuri'a, tabbas shine sarki idan ana maganar zabe.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu, hadimin shugaban kasa na musamman kan watsa labarai ya fitar, shugaban kasar ya ce:

"Wannan shaida ne da ke nuna dimokradiyyarmu ta girma kuma masu jefa kuri'a sun waye. Abin da ya bani mamaki shine talaka wanda galibi ana raina shi ya nuna cewa ya fahimci siyasa. A koyaushe ana zaton idan kayi shekara takwas a gwamna za ka tafi majalisa ka karasa aikin ka. Babu wanda ya isa ya raina masu jefa kuri'a a Najeriya yanzu. Siyasa za ta kara wahala, daga yanzu."

Kara karanta wannan

"Dimukradiyya Ce Tsari Mafi Dacewa", Buhari Ya Fada Wa Jakadu A Sakon Bankwana

Gwamnoni da suka gaza cimma burinsu na zuwa majalisa

Idan za a iya tunawa, gwamnoni masu ci - Okezie Ikpeazu na Abia, Samuel Ortom na Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Simon Lalong na Plateau, Darius Ishaku na Taraba, Ben Ayade na Cross Rivers da Abubakar Bagudu na Kebbi duk sun sha kaye a zaben neman zuwa majalisar dattawa.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, na APC shima ya gaza samun damar zarcewa kan kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164