Zababben Gwamnan APC Yayi Kus-Kus Da Shugaba Buhari, Ya Ce Jiharsa Na Neman Dauki
- Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Benue a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Hyacinth Alia, ya sanya labule da shugaba Buhari
- Mr Hyacinth ya koka kan halin da jihar sa ta Benue ta tsinci kanta inda yake cewa jihar na cikin tsaka mai wuya
- Zaɓaɓɓen yace akwai gagarumin aiki a gaban shi wajen dawo da jihar kan turba amma yana fatan ya samu nasarar yin hakan
FCT, Abuja- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya sanya labule da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a fadar shugaban ta Aso Villa a birnin tarayya Abuja.
Da yake tattaunawa da ƴan jaridar fadan shugaban ƙasa bayan kammala sanya labule da shugaba Buhari, Mr Alia ya koka kan halin da fannin aikin gwamnatin jihar Benue ya ke ciki, Premium Times ta rahoto.
A cewar sa, ɓangaren ma'aikatan jihar ya kusa ɗurkushewa inda yake cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai, amma zai dawo da martabarsa, rahoton Leadership.
Mr Alia ya yi nuni da cewa jihar na da bashin kuɗin albashi, fansho da garatuti sannan ya yi fatan mayar da hankali wajen magance ɗumbin matsalolin da zai tarar idan ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
Abin akwai takaici yadda ɓangaren aikin gwamnatin jiha ya kusa durƙushewa, yana cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai, saboda haka ina buƙatar kama aiki domin farfaɗo da shi ya cigaba da aiki."
“Muna da tulin bashin da a ba biya ba na albashi, fansho da gratuti. Don haka akwai abubuwa da yawa a gabana da zan mayar da hankali akai sannan ina da fatan cewa zan samu damar yin hakan."
Zaɓaɓɓen gwamnan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya yabawa shugaba Buhari kan hukuncin da ya yanke na tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe a ƙasar nan.
Sanatan APC Ya Yi Kus-Kus da Buhari a Aso Villa, Ya ce Zai Zama Shugaban Majalisa
A wani labarin na daban kuma, sanatan APC ya sanya labule da shugaba Buhari a Villa, yace shugabancin majalisar dattawa ta 10 da shi ya dace.
Sanata Osita Izunaso yace shugabancin majalisar dattawan yankin Kudu maso Gabas yakamata a. Miƙa shi.
Asali: Legit.ng