Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa, Ya Bayyana Wadanda Suka Janyowa Jam'iyyar Rashin Nasara a Kano

Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa, Ya Bayyana Wadanda Suka Janyowa Jam'iyyar Rashin Nasara a Kano

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya zargi wasu ƴaƴan jam'iyyar da laifi a jihar Kano
  • Shugaban jam'iyyar yace son zuciyar su ne ya sanya jam'iyyar ta faɗi ƙasa ba nauyi a jihar Kano
  • Abdullahi Adamu ya tabbatar da cewa jam'iyyar zata yi hukuncin da ya dace ga duk waɗanda suka sanya ta samu naƙasu

Abuja- Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana dalilan da suka sanya jam'iyyar tayi rashin nasara a jihar Kano.

Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da jaridar BBC Hausa.

Abdullahi
Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa, Ya Bayyana Wadanda Suka Janyowa Jam'iyyar Rashin Nasara a Kano Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Jam'iyyar APC a jihar Kano tayi rashin nasara a zaɓen shugaban ƙasa a hannun jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Sannan a zaɓen gwamnan jihar, ɗan takarar jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya kayar da takwaransa na jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna, bayan ya samu mafiya yawan ƙuri'u.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Kulla-Kullar Da Ake Shirya Masa Don Hana Shi Zuwa Kotu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka kuma ba iya nan kawai rashin nasarar jam'iyyar ta tsaya ba a jihar Kano, jam'iyyar ta rasa mafiya yawan kujerun ƴan majalisar tarayya na jihar a hannun NNPP, inda a kujerun sanata jam'iyyar APC ta samu ta tsira da guda taya tak.

Da yake tsokaci kan wannan rashin nasarar ta jam'iyyar APC a jihar, Adamu ya bayyana cewa akwai takaici yadda jihar Kano ta suɓuce daga hannun jam'iyyar ta su, inda yace hakan abin baƙin ciki ne.

Shugaban ya kuma nuna ƴatsa kan wasu jiga-jigan jam'iyyar a jihar a matsayin waɗanda suka janyo mata rashin nasara a jihar.

"Babban abin baƙin ciki ne ace wai mun rasa Kano." Domin Kano tana daga cikin jihohin da muke bugun ƙirji muce namu ne, don duk abinda zamu yi tana kan gaba-gaba. Gashi yanzu an zo an sanya ƴaƴan jam'iyya cikin baƙin ciki bayan sun gama duk abinda za su iya yi."

Kara karanta wannan

Da walakin: Bayan faduwar Kwankwaso, shugaban NNPP ya yi murabus, ya fadi dalili

Da aka tambaye sa ko su waye ke da alhaki kan kayen da jam'iyyar ta sha sai ya kada baki yace:

"Dole laifin wani ne mana, dole akwai laifi a cikin tafiyar nan, akwai masu laifi a ciki, akwai waɗanda ba suyi abinda yakamata ace sun yi ba."
"Amma saboda son zuciya gashi yanzu an sanya mu cikin wani hali don bai kamata ace mun samu wahalar shan wuya wajen cin Kano ba ballantana ace mun faɗi, amma komai ya samu bawa da sanin ubangijin shi, idan wannan abun muƙaddari ne to bamu da maganin shi."

Abdullahi Adamu ya kuma tabbatar da cewa idan ƙurar zaɓe ta gama lafawa, jam'iyyar zata hukunta duk waɗanda suka yi mata ba daidai ba a lokacin zaɓe.

Wata Kungiya Ta Bayyana Wanda Ya Cancanci Matsayin SGF a Gwamnatin Tinubu, Ta Bayar Da Dalilanta

A wani labarin na daban kuma, wata ƙungiya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ta shawarci Tinubu yaba Simon Lalong muƙamin SGF a gwamnatin sa.

Ƙungiyar ta bayyana dalilan da ya sanya Lalong ya dace ya samu wannan kujerar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng