Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Wata Makarkashiya Da Ake Hada Masa
- Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers, ya koka kan rashin adalcin da ake musu
- Tonye Cole ya bayyana cewa da gangan ake son hana su ƙalubalantar sakamakon zaɓen gwamnan jihar a kotu
- Ɗan takarar gwamnan ya zargi hukumar zaɓe ta INEC da rashin basu haɗin kan da ya dace
Jihar Rivers- Ɗan takarar gwamnan jihar Rivers a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Tonye Cole, yace ana yiwa jam'iyyar sa zagon ƙasa domin hana ta ƙalubalantar sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Da yake magana ranar Litinin a yayin tattaunawa da gidan talbijin na Channels Tv, Cole yace harin da aka kai wa ƴaƴan jam'iyyar wani shiri ne domun ɓata wa jam'iyyar lokaci kan ƙarar zaɓen. Rahoton The Cable
Ɗan takarar na jam'iyyar APC, ya bayyana cewa jam'iyyar sa bata samu haɗin kan da take buƙata ba daga wajen hukumar zaɓe ta INEC dangane da kayayyakin zaɓen.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Alamu sun nuna akwai wata maƙarkashiya domin hana mu kai ƙara mai inganci a gaban kotu."
“Ko dai an hanu samun takardun CTC waɗanda muke buƙafa domin haɗa ƙarar mu ko da gangan ake hana mu ta yadda lokaci zai ƙure mana."
"Dukkanin biyun ɗanjuma ne da ɗanjummai. Da farko an cafke lauyoyin mu. Dukkanin hujjojin da muka haɗa an tafi da su. Mun shafe Asabar da Lahadi muna ƙoƙarin dawo da su."
“Mun samu mun dawo da su ranar Lahadi. Ranar mun kwashe lokacin wajen samo takardu. Ba a bamu takardun ba, a maimakon hakan, sai muka ƙara da shan harbi, tsangwama, jifa da raunika."
“Wata rana (Litinin) ta ƙara wucewa. A yaushe ne zasu samu lokacin shirya ƙarar da dole zamu miƙa ta?"
"Bamu samu haɗin kai da muke buƙata daga wajen INEC ba ko kaɗan. Na rasa gane meyasa INEC tayi shiru. Meyasa kwamishinan zaɓe na INEC baya ɗaukar kira na?"
Ɗan takarar ya nuna ƙwarin guiwar sa kan cewa wannan maƙarƙashiyar da ake ƙulla musu ba zata kai ga ci ba. Rahoton Naija News
Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Wasu Manyan Jiga-Jiganta a Jihar Edo
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta dakatar da wasu manyan ƴaƴan ta a jihar Edo, daga jam'iyyar.
Dakatarwar ta biyo zarge-zargen da ake musu na cin dunduniyar jam'iyyar a lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng