Wasu Matasa Sun Kunno Wuta Suna Neman a Soke Zaban Sanata Mace a Abuja
- Bayan ta samu lashe zaɓen sanata, wasu matasan na son a soke zaɓen sanatan birnin tarayya Abuja
- Matasan a ƙarƙashin wata ƙungiya na son a soke zaɓen ne saboda a cewar su, an tafka kura-kurai sosai a cikin sa
- Sun kuma yi kiran da ake sabon zaɓen a kujerar sanatan ta birnin tarayya Abuja domin ba mutane ƴancin zaɓar wanda suke so
Abuja- Wasu matasa a ƙarƙashin ƙungiyar Concerned FCT Youth Group (CFYG) sun yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta soke zaɓen sanatan birnin tarayya Abuja.
Matasan na neman hukumar INEC da ta soke nasarar da ƴar takarar jam'iyyar Labour Party (LP), Ireti Kingibe, ta samu a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton Daily Trust
Da yake tattaunawa da ƴan jarida ranar Litinin a birnin tarayya Abuja, Kwamared Alhassan Danjuma, yace aniyar su ta son ganin an soke sakamakon zaɓen ta samu ne a dalilin ɗumbin kura-kuran da aka tafka a zaɓen.
Yace akwai rahotannin wurare da yawa inda aka hana mutane kaɗa ƙuri'un su a cikin ƙananan hukumomi shida na birnin tarayyar. Rahoton Blueprint
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya cigaba da cewa:
"A bisa dalilin hakan ne ƙungiyar Concerned FCT Youth Group, bayan kammala binciken ta, take tattaunawa da ƴan jarida domin bayyanawa da babbar murna cewa zaɓen sanatan FCT na ranar 25 ga watan Fabrairu akwai kura-kurai a cikin sa."
"Bayan kura-kuran da aka tafka sannan an hana mutane da dama kaɗa ƙuri'un su. Hakan ya sanya muke kira ga INEC da ta soke zaɓen."
Daga nan kuma sai yayi kira kan hukumar zaɓen ta INEC da ta sake sabon zaɓe, a kujerar sanatan FCT wanda zai ba mutane damar zaɓar wanda ran su yake so.
Ribas Zata Goyi Bayan Wanda APC Ke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai, Wike
A wani labarin na daban kuma, gwamna Wike na jihar Rivers ya bayyana cewa jihar zata marawa duk wanda jam'iyyar ke son ya zama sugaban majalisar wakilai ta 10 baya.
Wike yayi wannan jawabin ne yayin da wani ɗan majalisar APC mai neman shugabancin kujerar ya kai masa ziyara.
Asali: Legit.ng