APC ta Bude Kofar Rikici da Korar Mataimakin Shugaban Majalisa da Tsohuwar Hadimar Buhari

APC ta Bude Kofar Rikici da Korar Mataimakin Shugaban Majalisa da Tsohuwar Hadimar Buhari

  • Wasu sun fito sun bada sanarwar korar Sanata Ovie Omo-Agege daga jam’iyyar APC a Delta
  • Wadannan mutane da ke ikirarin zama shugabannin APC sun zargi ‘dan takaran da laifuffuka
  • Jam’iyyar APC ta kasa da ofishin yakin neman zaben Omo-Agege sun yi watsi da maganar korar

Delta - Rigimar da ake fama da ita a jam’iyyar APC ta kara jagwalgwalewa da korar Sanata Ovie Omo-Agege da wasu ‘ya ‘yanta suka yi a jihar Delta.

Wani rahoto da ya fito a jaridar Tribune ya ce takardar korar Ovie Omo-Agege daga APC ta fito ne daga Hon. Isaac Ulebor da sunan shugaban jam’iyya.

Isaac Ulebor yake cewa sun dauki matakin sallamar mataimakin shugaban majalisar dattawan daga jam’iyya mai-ci bayan taron shugabanni da aka yi.

Hon. Ulebor yake cewa shugabannin APC na mazabar Orogun a karamar hukumar Ughelli ta Arewa sun yi zama kan batun a ranar 20 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida da ‘Yan takara 3 da Aka Gwabza da Su Kafin Lashe Zaben Gwamna

Laifin da ke wuyan Ovie Omo-Agege

A cewarsa, jam’iyya ta kafa hujja da sassa na 21.2 (I)(Ii)(vii) 21.3 da 21.5(g) wajen sallamar Ovie Omo-Agege, yanzu bai cikin ‘ya ‘yan APC a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin Shugaban Majalisa
Ahmad Lawan, Muhammadu Buhari da Ovie Omo-Agege Hoto: factualtimesng.com
Asali: UGC

Saboda haka an kori Ovie Omo-Agege a matsayin ‘dan jam’iyya ba tare da bata lokaci saboda laifuffuka da-dama da kuma yi wa jam’iyya zagon-kasa.
Sannan ya yi aika-aikar da ta jawowa jam’iyya abin kunya a jihar, wanda hakan ya yi tasiri a zabe.

- Isaac Ulebor

An kori Lauretta Onochie

Rahoton ya ce wannan na zuwa ne a lokacin da aka kori tsohuwar hadimar shugaban kasa kuma shugabar NDDC, Lauretta Onochie daga jam’iyya mai-ci.

Ana jefi Onochie da zargin yi wa PDP aiki a zaben da ya gabata. Haka zalika wadannan shugabanni sun ce Cairo Ojougboh ya tashi daga zama ‘Dan APC.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Rantsar da Sabon Shugaban Kasa, Wata Jam’iyya Ta Kai Tinubu Kotu

Ba za ta sabu ba - APC, Niboro

Amma Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka ya shaidawa Vanguard cewa ba su san da zaman wadannan shugabanni na reshen jihar Delta ba.

Kakakin jam’iyyar na kasa ya ce uwar jam’iyya ba ta aiki da ‘yan tawaren da suka fitar da wannan sanarwa, don haka har gobe Sanatan yana nan a jam'iyya.

‘Dan takarar Gwamnan ya karyata korarsa da ake cewa an yi, ya yi magana ta bakin Ima Niboro.

Siyasar 2023

A wani rahoto, kun ji za a iya cewa Mohammed Bago, Umar Namadi, Dikko Radda, da Hyacinth Alia sun ci zabe cikin sauki a karkashin jam'iyyar APC a 2023.

Amma a Zamfara, Kano da Bauchi, Jam’iyyun adawa sai da suka yi da gaske kafin su doke APC. PDP ta zarce a Bauchi, ta karbe Zamfara, NNPP talashe Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng