Yan Sanda Sun Mamaye Sakatariyar Jam'iyyar Labour Party a Imo
- Jami'an hukumar 'yan sanda sun mamaye sakatariyar LP a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya yau Litinin
- Sakataren LP na kasa, Umar Farouk, ya koka cewa wannan ne karo na biyu a cikin wata ɗaya da ya shige
- Ya ce sun nemi jin meyasa a ofishin IGP amma aka faɗa musu ba bu wani umarni makamancin haka
Imo - Rundunar 'yan sanda ta kwace babbar Sakatariyar jam'iyyar Labour Party reshen jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Sakataren LP na ƙasa, Umar Farouk, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 3 ga watan Afrilu, 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto Sanarwan na cewa:
"Uwar jam'iyyar LP ta ƙasa ta kaɗu da samun labarin mamaya da kuma kwace Sakatariyarta da ke Owerri, yau Litinin 3 ga watan Afrili, 2023. Hakan ya biyo bayan wanda ya faru ranar Laraba 15 ga watan Afrilu."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sakataren LP ya kara da cewa gwamnatin Imo ta jam'iyyar APC ta ce an ɗauki wannan matakin ne saboda cika umarnin Kotu.
"Amma har kawo yanzu babu wani umarnin Kotu da aka kawo mana, babu wani umarni da aka turo mana ko wakilin Kotu ya kawo, haka 'yan sandan da suka mamaye wurin ba su nuna mana umarnin ba."
"A halin da ake ciki, jami'anmu da ma'aikata baki ɗaya basu da ikon shiga Sakatariyar. Mun tuntuɓi ofishin Sufetan 'yan sanda kan lamarin kuma an tabbatar mana babu wani abu da zai sa a kwace wurin."
- Umar Farouk.
Sakataren ya ƙara da cewa rundunar yan sanda ta sanar da LP cewa ba ta tura jami'inta ko ɗaya zuwa Sakatariyar Labour Party ba a jihar Imo.
Farouk ya roki mambobin LP da magoya baya a jihar su ƙara hakuri duk wannan buta da ƙullin da ake masu a halin yanzu, kamar yadda Leadershi ta ruwaito.
An Gano Sunayen Mutum 3 da Tinubu Ke Shirin Ba Manyan Muƙamai
A wani labarin kuma Sabbin bayanai sun fallasa sunayen mutun uku dake sahun gaba a samun manyan muƙamai a gwamnatin Bola Tinubu.
Wasu majiyoyi sun ce Tinubu ya rubuta sunan waɓda yake son naɗawa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da kuma tawagar tattalin arziki.
Asali: Legit.ng