Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Ribas, Cole, Ya Tsallake Rijiya da Baya
- Ɗan takarar gwamna a inuwar APC a jihar Ribas, Tonye Cole, ya shallake rijiya da baya a ofishin hukumar zaɓe INEC
- Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne lokacin da Mista Cole ya je hedkwatar INEC domin duba takardun sakamakon zaɓe
- Jami'an tsaron da ke gadin ɗan takarar ne suka yi kokarin janye shi daga wurin suka maida shi Sakatariyar APC a Patakwal
Rivers - Ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar APC a jihar Ribas, Tonye Cole, wanda ya yi rashin nasara a zaben da aka kammala, ya tsallake rijiya da baya.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa wasu miyagun 'yan daban siyasa ne suka farmaki Mista Cole a Titin GRA Junction, da ke Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa yan daban sun kuma farmaki jami'an tsaron da ke gadin ɗan takarar gwamnan da kuma Motocin ayarinsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Cole na hanyar zuwa hedkwatar hukumar zaɓe (INEC) domin cika yarjejeniyar da ya cimma da kwamishinan zaɓe (REC) na Ribas, Johnson Sinikiem.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ɗan takarar da shugaban INEC na jihar Ribas sun cimma matsayar cewa zai zo ya duba sahihan takardun sakamakon babban zaɓen gwamna da yan majalisun jiha da aka gudanar a jihar.
Lokacin da yake zantawa da 'yan jarida jim kaɗan bayan ya ziyarci INEC ranar Jumu'a da ta shige, Cole, ya ce ya tattauna da Sinikiem kuma ya tabbatar masa sakamakon zaɓen zai haɗu ranar Litinin.
Jami'an tsaro sun taka rawa wajen ceton ɗan takarar gwamna
Bayanai sun nuna cewa domin daƙile munin lamarin, jami'an tsaron da ke gadin ɗan takarar suka yi gaggawar janye shi daga nufin tsagerun 'yan daban suka maida shi Sakatariyar APC.
A wani labarin kuma Tsohon Gwamna Kuma Fitaccen Sanatan APC Ya Yi Babban Rashi a Iyalansa
Uwar gidan tsohon gwamnan Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya, Sanata Orji Uzo Kalu, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekara 61 a duniya.
Sanata Kalu ya ce za'a gudanar da bikin tunawa da ita na musamman a ƙasar Amurka.
Asali: Legit.ng