Kotu Ta Mayar Da Tsigaggen Kakakin Majalisar Dokokin Plateau Kan Kujerar Sa
- Kotu ta mayar da tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar Plateau kan muƙamin sa
- Kotun ta kuma hana kakakin majalisar dokokin jihar na yanzu kiran kan sa a matsayin shugaban majalisar
- Tun a cikin shekarar da ta gabata ne dai aka tsige Hon. Nuhu Ayuba Abok a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Plateau
Jihar Plateau- Wata babbar kotun jihar Plateau, a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Nafisa Musa, a ranar Litinin ta mayar da tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Nuhu Abok, a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƴn majalisar dokokin jihar sun tsige Hon. Nuhu Abok ne a ranar 28 ga watan Octoban 2021.
Sai dai, Abok ya garzaya gaban babban kotun jihar domin ƙalubalantar hukuncin ƴan majalisar na tsige shi daga kan muƙamin sa.
A cikin hukuncin ta kotun ta tabbatar shaidun da masu shigar da ƙara suka gabatar inda tace ba a tsige ɗan majalisar bisa ƙa'ida ba, a dalilin hakan ta soke tsigewar da aka yi masa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotun ta kuma umurci waɗanda ake ƙara ɗa su bayar N1.5m kuɗin zuwa kotu da N138,000 a matsayin kuɗin shigar da ƙarar.
Kotun ta kuma hana kakakin majalisar dokokin jihar na yanzu, kiran kansa a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar. Rahoton Ait Live
Idan ba a manta ba dai, bayan an tsige Abok daga kan muƙamin sa, Hon. Yakubu Sanda, ya maye gurbin sa a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar.
Sai dai, Hon. Sanda ya sha kashi a hannun ƴar takarar jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Hon. Mrs. Happiness Matthew Akawu, a mazaɓar Pengana, a zaɓen majalisar dokokin jihar dana gwamna da aka kammala kwanan nan.
Kotun ƙoli tayi Fatali da Ƙarar Nwajiuba dake Fatan Ta Nuna Rashin Cancantar Takarar Tinubu da Atiku
Gwamna Wike Ya Bukaci 'Yan Adawar Jihar Rivers Su Marawa Zababben Gwamnan Jihar Baya
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Rivers ya aike da muhimmin saƙo zuwa ga ƴan adawar da suka sha kashi a zaɓen gwamnan jihar.
Gwamna Nyesom Wike ya nemi ƴan adawar da su zo a haɗa kai da su domin ciyar da jihar ta Rivers gaba.
Asali: Legit.ng