"Sun Fara Siyan Ta Da Kudi" Sanatan APC Ya Magantu Kan Shugabancin Majalisa Ta 10
- Sanata Ali Ndume ya koka kan yadda aka fara amfani da kuɗi domin samun shuagabancin majalisa
- Sanatan ya bayyana cewa tuni har wasu ƴan siyasa suka fara raba kuɗaɗe domin samun shugabancin majalisun
- Ali Ndume yana son a kafa wata doka wacce zata hukunta masu dukiyar da ba zasu iya bayanin yadda suka samo ta ba
Abuja- Ɗan majalisa mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, yace ƴan siyasa sun fara siyan shugabancin majalisa ta 10 wacce ba a kai ga rantsar da ita ba.
Ndume, wanda aka tattauna da shi a gidan talbijin na Channels Tv a shirin su na 'Sunday Politics' ya bayyana cewa da yana da kuɗi da shi ya zama shugaban majalisar dattawa a shekarar 2023.
Sanatan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya kwashe shekara 20 a majalisa, yana son a kafa dokar dukiyar da ba a san yadda aka samo ta ba domin hukunta gurɓatattun ƴan siyasa waɗanda ke da dukiya mai alamar tambaya.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yakamata ace akwai dokar nan saboda idan ka nuna dukiya wacce tafi abinda kake samu, sai a bincike ka sannan dukiyar a ƙwace ta sannan idan tayi yawa sosai, sai ka fuskanci tuhuma."
"Yanzu kaga abinda yake faruwa. Shugabanci a ƙasar nan ya koma wajen ɓarayi da masu siya da kuɗin su. Babu wata dimokuraɗiyya a ciki.
“Tuni har sun fara siyan ta. Shin baka ji cewa bane sun fara rarraba kuɗi? Sannan ina tunani a wancan zaɓen, da ina da kuɗi da nayi nasara. Bani da kuɗi."
Jam'iyyar APC ta lashe kujeru masu rinjaye na kujerun majalisu a zaɓen inda ta samu kujeru 55 cikin 109 na majalisar dattawa da kujeru 160 cikin 360 na majalisar wakilai.
Jiga-jigan jam'iyyar APC da dama sun nuna aniyar su tayin takarar shugabancin majalisun biyu. Daga cikin su akwai Orji Kalu, Jibrin Barau, Godswill Akpabio, Dave Umahi, Ahmad Lawan, Abdulaziz Yari, Osita Izunaso, da sauran su.
Sai dai har ya zuwa yanzu jam'iyyar bata yi magana ba kan shugabancin majalisar. Shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu ya bayyana cewa jam'iyyar bata tsara yankin da shugabannin majalisar zasu fito ba. Rahoton New Telegragh
Sanatan Jihar Kano Ya Shiga Sahun Masu Neman Kujerar Majalisar Dattawa a 2023
A wani labarin na daban kuma, sanatan jihar Kano ya shiga cikin jerin sahun masu neman shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Sanata Jibrin Barau Maliya ya bayyana aniyar sa ta samun shugabancin majalisar.
Asali: Legit.ng