Gwamnatin Wucin Gadi: Ina Hango Bikin Rantsarwa Na Gudana Duk Da Magudin Zabe” - Ayodele
- Fitaccen faston Najeriya mazaunin Lagas ya yi hasashe game da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
- Gabannin ranar 29 ga watan Mayu, malamin addinin ya ce za a yi bikin duk da kulla-kullan da wasu yan siyasa ke yi na kafa gwamnatin wucin gadi
- Malamin addinin ya ci gaba da bayyana cewa ba za a sauya ranar bikin ba kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga magajinsa
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya yi sabon hasashe gabannin bikin mika mulki ga sabuwar gwamnati na ranar 29 ga watan Mayu.
Ayodele ya ayyana cewa ba za a kafa gwamnatin wucin gadi ba a Najeriya kuma babu abun da zai hana bikin rantsarwar a Najeriya, Nigerian Tribune ta rahoto.
Ba za a kafa gwamnatin wucin gadi ba, Ayodele ya yi sabon hasashe
A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya bayyana cewa duk da tangarda a zaben, babu wani abu mai kama da gwamnatin wucin gadi da za a kafa saboda Allah bai nuna masa abu mai kama da hakan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa abun da ya gani shine cewa ranar bikin rantsarwar ba zai sauya ba kuma cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga wanda ya kamata ya mikawa.
Malamin ya ce:
"Duk da tangardar, Bana ganin wani abu da zai hana bikin rantsarwar ko wani abu mai kama da gwamnatin wucin gadi."
Primate Ayodele ya ce hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ce ta haddasa rikici da tashin hankalin da ake fuskata a kasar saboda magudin zabe da aka yi a watan Fabrairu, rahoton Daily Post.
“Ba Za a Rantsar Da Tinubu Ba:” Magoyin Bayan Peter Obi Ya Fasa Ihu a Bidiyo, Ya Hana Jirgin Sama Tashi
Ba za a rantsar da Tinubu ba, Masoyin Peter Obi ya kawo tangarda ga tashin jirgin sama
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa wani dan gani-kashenin Peter Obi na Labour Party ya haddasa wata yar dirama a cikin jirgin sama yayin da suke shirin tashi daga Abuja zuwa Lagas.
Ana gab da tashi, sai mutumin ya kurma ihu cewa ba za a rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu ba, cewa ba shine ya ci zaben watan Fabrairu ba.
Asali: Legit.ng