APC Ta Fatattaki Tsohon Jigonta Na Kasa A Bauchi, An Bayyana Laifin Da Ya Aikata

APC Ta Fatattaki Tsohon Jigonta Na Kasa A Bauchi, An Bayyana Laifin Da Ya Aikata

  • Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Bauchi ta kori tsohon jigonta wanda ya taba wakiltar jihar a matakin kasa, Sirajo Dada, kan cin amanar jam'iyya
  • An kori Dada ne sakamakon matakin da shugabannin jam'iyyar APC suka cimma yayin taron da suka yi a karamar hukumar Gamawa na jihar Bauchi
  • Yayin da ya ke sanar da korar Dada daga jam'iyya, Ahmed Saleh Super, ciyaman din jam'iyyar APC a karamar hukumar Gamawa, ya ce abu ne mai wahala amma ya zama dole

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Bauchi ta kori Sirajo Dada, tsohon jami'inta na kasa da ke wakiltar jihar Bauchi daga jam'iyya a karamar hukumar Gamawa kan ayyukan cin amanar jam'iyya.

A cewar The Tribune, an yanke shawarar korarsa ne yayin wani taron gaggawa na shugabannin APC a karamar hukumar Gamawa a ranar Asabar 1 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Jigon APC Ya Ce Peter Obi Ba Zai Yi Nasara A Kotu Ba, Ya Bada Dalili

Jiga-jigan APC.
APC ta kori fitaccen jigonta a Bauchi. Hoto: Photo Credit: APC Nigeria
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa APC ta kori tsohon jigonta na kasa a jihar Bauchi

Ahmed Saleh Super, shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Gamawa, ya sanar da korar a sakatariyar jam'iyyar da ke karamar hukuma.

Super ya ce matakin wahala ne ga shugabannin jam'iyyar, amma shine abin da ya fi dacewa domin jam'iyyar ta nuna ladabatarwa.

A cewar Super:

"Tabbas Sirajo Dada ya yi aiki don kayar da jam'iyyar APC a karamar hukumar yayin babban zaben shekarar 2023. An kama shi yana bata wa yan takarar APC suna."

Bayannan baya-baya kan APC, Bauchi, Zaben 2023

Ya yi ikirarin cewa Dada ya saba matsayar jam'iyyar ta APC ta hanyar yi wa dan takarar jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP, na kujerar majalisar wakilai na tarayya kamfe.

Shugabannin jam'iyyar APC sun gargadi Dada kan abin da ya ke aikatawa amma ya ki sauraronsu.

Kara karanta wannan

An Fara Diraman Bayan Zabe A LP Yayin Da Jam'iyyar Ta Dakatar Da Jiga-Jiganta 11 A Fitaccen Jihar Arewa

Duk da cewa jam'iyyar APC ta lashe zaben majalisar wakilai na tarayya da na shugaban kasa a mazabar, abin da Dada ya aikata ya shafi nasarar jam'iyyar a zaben sanata a yankin.

Ganduje ya gargadi Abba Gida-Gida, ya ce ya jira a rantsar da shi kafin ya fara bada umurni a Kano

A wani rahoton, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ja kunnen zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya dena saki baki kan harkokin mulkin jihar domin ba a riga an rantsar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164