Gwamnatin Delta Ta Kori Manyan Hadiman Gwamna 6 Kan Muhimmin Abu

Gwamnatin Delta Ta Kori Manyan Hadiman Gwamna 6 Kan Muhimmin Abu

  • Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya tsige manyan hadimansa na siyasa daga kan muƙamansu kan zargin rashin ɗa'a
  • Hakan na kunshe a cikin wata wasika da Sakataren gwamnatin Delta ya aike wa babban mai baiwa gwamna shawara kan abinda ya shafi siyasa
  • Sanarwan ta ce matakin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2023 kuma ta bayyana sunayen waɗanda aka kora

Delta - Gwamnatin jihar Delta karkashin jagorancin gwamna Ifeanyi Okowa ta sallami manyan hadimai 6 daga bakin aiki kan wasu halayen rashi'a ɗa'a da suka yi a bainar jama'a.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wannan matakin na kunshe ne a wata wasiƙa da Sakataren gwamnatin jihar, Chief Patrick Ukah, ya aike wa babban mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa.

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
Gwamnatin Delta Ta Kori Manyan Hadiman Gwamna 6 Kan Muhimmin Abu Hoto: Ifeanyi Okowa
Asali: Facebook

Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Maris, 2023, ta ce an kori hadiman daga bakin aike ne bisa ɓanɓarma da rashin riƙe sirrin kudirorin gwamnati mai ci.

Kara karanta wannan

Jam'iyya Ta Bi Sahun PDP, Ta Dakatar da Shugabanta Na Ƙasa Kan Muhimmin Abu, Rigima Ta Kaure

Haka zalika gwamnatin ta bayyana cewa matakin tunbuƙe su daga kan muƙamansu zai fara aiki ne daga ranar Asabar, 1 ga watan Afrili, 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jerin sunayen hadiman da aka soke naɗinsu a gwamnatin Delta

Waɗanda gwamnatin ta ɗauki matakin kora daga aiki sun haɗa da, Onwuka London, Victor Ossai, Iyasele Tunji (SSA), da Ramon Ossai (SA).

Sauran hadiman da lamari ya shafa su ne, Lawrence Odu (SA) da kuma Mista Tobechukwu Richard Ukwamedua (SSA).

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar PDP ta maye gurbin shugaban jam'iyya na kasa bayan Kotu ta ba da umarni.

Gwamna Okowa na jihar Delta ne ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023 karkashin inuwar PDP, wanda Bola Tinubu ya samu galaba.

A wani labarin kuma Zababben Gwamna Zai Bullo Da Sabuwar Dabarar Yakar Yan Ta'adda a Katsina

Kara karanta wannan

Ana Saura Wata 2 Cikar Wa'adin Mulkin Sa, Wani Babban Ministan Buhari Yayi Murabus

Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, gwamnan jihar Katsina mi jiran gado ya kai ziyara ga shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari, a birnin tarayya Abuja.

Sabon gwamnan ya bayyana sabon tsarin da zai bullo da shi domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a faɗin jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262