Abba Gida-Gida: Ba Zan Biya Duk Wani Bashi Da Ganduje Ya Ciwo Wa Kano Bayan Zabe Ba

Abba Gida-Gida: Ba Zan Biya Duk Wani Bashi Da Ganduje Ya Ciwo Wa Kano Bayan Zabe Ba

  • Gwamna mai jiran gado a Jihar Kano ya gargadi masu bayar da bashi ga gwamnatin Kano da su dakata daga yanzu har zuwa lokacin rantsuwa
  • Abba Kabir Yusuf wanda ake yi wa lakaci da Abba Gida-Gida ya ce gwamnatinsa ba zata lamunci duk wani bashi da gwamnatin Ganduje ta karba bayan zabe ba
  • Wata sanarwa da sakataren yada labaran zababben gwamnan ya fitar daren Juma'a ta ce, a guji bayar da bashi ga gwamnati mai ci ba tare da sanin gwamnati mai jiran gado ba

Jihar Kano - Zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, (Abba Gida-Gida) ya sake gargadar kafanin masu bayar da bashi da lamuni ga gwamnatin Kano da su dakata, rahoton The Punch.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran zababben gwamnan ya fitar a daren Juma'a, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce, daga ranar 18 ga watan Maris zuwa 29 ga watan Mayu, kada wani mai bayar da bashi (gida da waje) ya sahale ko ya bayar da bashi ga gwamnatin Kano ba tare da ya tuntubi gwamnati mai jiran gado ba.

Kara karanta wannan

"Mara Amfani" Ganduje Ya Fusata, Ya Maida Zazzafan Martani Ga Abba Gida-Gida Kan Karɓo Bashi

Abba Kabir Yusuf
Ba zan biya bashin da Ganduje ya karbo bayan zabe ba, in ji zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Abba Gida-Gida ya gargadi masu ba wa gwamnatin Kano bashi

Idan za a iya tuna wa zababben gwamnan ya fitar da makamanciyar sanarwar inda ya ke shawartar mutane, kungiyoyi da masana'antu da su dakatar da duk wani gine-gine a wuraren gwamnati ba tare da bata lokaci ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce, duk bashin da aka bawa gwamnatin Kano daga lokacin da aka gudanar da zabe zuwa rantsuwa ba tare da sani da amincewar gwamnati mai jiran gado ba, gwamnati mai jiran gado ba zata amince da shi ba.
"Duk masu bayar da bashi ga gwamnatin Kano su sani cewa duk dokoki da dalilan bashin da aka riga aka karbo gwamnati mai zuwa zata sake duba yadda aka kashe kowane bashi.
"An fitar da shawarar ne saboda bukatar al'umma, a kula, in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a Zamani 1: Har Gobe Ni Ne Gwamnan Kano – Dr. Ganduje ga Abba Gida Gida

Har yanzu ni ne gwamnan jihar Kano, Ganduje ya gargadi Abba Kabir Yusuf

Tunda farko kun ji cewa gwamnan Kano mai barin gado Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi Abba Kabir Yusuf, gwamna mai jiran gado ya dena saka baki kan mulkin jihar a yanzu.

Gandujen ya tunatar da zababben gwamnan cewa shine gwamnan Kano har zuwa ranar 29 ga watan Mayu don haka ba shi da ikon bada umurni a abin da ke hurumin gwamnati ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164