Jam'iyyar LP Ta Dakatar da Shugabanta Na Kasa, An Fara Martani
- Jam'iyyar Labour Party ta bi sahun PDP, ta shiga sabon rikici kan kujerar shugabanta na ƙasa
- Shugabannin LP a matakin gunduma daga jihar Edo sun dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa, Julius Abure
- Sai dai labarin bai wa uwar jam'iyya ta ƙasa daɗi ba, nan take Sakatare ya fito ya maida raddi mai ɗumi
Edo - Labour Party (LP) reshen gunduma a jihar Edo ta dakatar da shugaban jam'iyya na kasa baki ɗaya, Julius Abure, bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.
Rahoton Daily Trust ya ce wannan dakatarwan na zuwa ne mako guda bayan gunduma a jihar Benuwai ta dakatar shugaban PDP, Iyirchia Ayu.
A wurin taron manema labarai, shugaban LP na gumduma, Martins Osigbemhe, ya ce shugabannin jam'iyya ne suka dakatar da Abure gabanin yanke hukuncin karshe kan ƙorafe-kirafen da ke kansa a Kotu.
Ba zai yuwu ba - Sakataren LP na ƙasa
Amma Sakataren jam'iyyar LP na kasa, Mallam Farouk Umar, ya yi fatali da batun inda ya bayyana shi da saɓa wa doka.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
"Sun ɗora zarge-zarge a kansa wanda ba gaskiya bane sharrri ne kawai na waɗanda suka kira taron yan jaridan. Muna ganin ya dace mu yi raddi kan abinda ya faru."
"Matasan da muka gani a wurin ba kowan kowa bane a Labour Party ta jihar Edo kamar yadda suka yi ikirari. Duk wani shugaba a matakin jiha, ƙaramar hukuma ko gunduma mun san shi."
"Ko ɗaya daga ciki bamu hanga ba a wurin, kawai wasu mutane ne suka ɗauki hayar wuri a Abuja aka cika musu aljihu suka karanta kalaman da aka tsara musu."
Ya ce kundin dokokin jam'iyyar LP bai bar komai ba game da wanda ke da hurumin dakatar da shugaban jam'iyya da wanda bai da iko, kamar yadda Channels ta ruwaito.
A wani labarin kuma Zababben gwamnan APC a Jihar Sakkwato ya roki PDP mai barin gado da sauran jam'iyyu abu 1
Ahmed Aliyu tare da mambobin majalisar dokokin jihar 30 su karbi shaidar cin zaɓe daga wurin hukumar zabe ta ƙasa (INEC).
A jawabinsa na wurin, zabbaben gwamnan na jam'iyyar APC ya ce ya shirya dawo da jihar Sakkwato kan turba mai kyau.
Asali: Legit.ng