Dattawan Arewa Sun Yi Gargadi Kan Zafafa Yanayin Siyasar Najeriya

Dattawan Arewa Sun Yi Gargadi Kan Zafafa Yanayin Siyasar Najeriya

  • Dattawan arewa sun magantu kan yanayin yadda abubuwa ke tafiya a kasar bayan zaben 2023 da ya gudana
  • Kungiyar NEF ta bukaci shugabannin jam'iyyu da su dakatar da masu magana da yawunsu daga yin kalamai masu cutarwa da ka iya zafafa yanayin da ake ciki
  • Manayan arewan sun bukaci yan Najeriya su kyale bangaren shari'a ya yi aikinsa cikin kwanciyar hankali da lumana

Kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga shugabannin jam'iyyun siyasa da su hana masu magana da yawunsu amfani da kalamai masu illa da cece-kuce da ka iya zafafa yanayin siyasar kasar.

A wata sanarwa da kakakin NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya saki a ranar Juma'a,31 ga watan Maris, kungiyar ta ce ta bi yadda tsarin zaben ya gudana, wanda har yanzu ana shiri ko gudanar da wasu daga cikinsu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Duk Da NNPP Ta Yi Nasara A Kano Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya

Kakakin kungiyar dattawan arewa yana jawabi
Dattawan Arewa Sun Yi Gargadi Kan Zafafa Yanayin Siyasar Najeriya Hoto: Punch
Asali: UGC

Daily Post ta nakalto Baba-Ahmed yana cewa:

"Don haka, kungiyar ta damu da zantuka da maganganu, wanda ya haifar da tashin hankali da cece-kuce da ke barazana ga dangantakar da ke tsakanin al'umma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya kamata shugabannin jam'iyya su dakatar da kakakinsu daga amfani da kalmomi masu cutarwa da musayar yawu."

Ku bar bangaren shari'a ya yi aikinsa, NEF ga yan Najeriya

Sai dai kuma, ya roki yan Najeriya da su bari bangaren shari'a ya sauke hakkin da ya rataya a wuyansa cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kungiyar ta nuna damuwarta cewa shugabanni basa sauke hakokkin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata don karfafawa mutane gwiwar mutunta tsarin shari'a, wanda yana da muhimmanci a tsarin zabe.

NEF ta kuma tunatar da bangaren shari'a cewa yan Najeriya na duba zuwa gareta don ceto damokradiyyarta da kuma dawo da karfin gwiwar yan Najeriya a kan mutunci da iyawarta.

Kara karanta wannan

IPAC Ta Yi Martani Yayin da DSS Ta Gano Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

Dan Obidient ya ce ba za a rantsar da Tinubu ba a bidiyo

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan gani-kashenin Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party a zaben da aka yi ya ce babu mai rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu.

Mutumin wanda ya kawo tsaico ga tashin jirgin sama na kamfanin Ibom ya ce sam ba Tinubu bane ya ci zaben da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng