Bayanai Sun Fito Yayin Da Shettima Ya Gana Da IBB, Abdusalami Gabanin Rantsar Da Tinubu
- Zababben shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi taron sirri da tsaffin shugabanin kasa biyu na mulkin soja daga jihar Neja
- A ranar Alhamis, Shettima ya gana da tsohon shugaban kasa na soja Ibrahim Badamasi Babangida da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar
- Da ya ke jawabi ga manema labarai bayan taron, Shettima ya ce dattawan kasar biyu ababen karfafa gwiwa ne ga kasa kuma gwamnatin Tinubu za ta bukace su
Minna - Sanata Kashim Shettima, zababben mataimakin shugaban kasa, ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida da tsohon shugaban kasa a zamani soja, Janar Abdulsalami Abubakar a Minna, babban birnin jihar Neja.
Tsohon gwamnan na jihar Borno ya kuma ziyarci Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Dalilin da yasa Shettima ya ziyarci IBB da Abdulsalami kafin rantsar da Tinubu
Da ya ke magana bayan ziyarar da ya kai wa dattawan kasar, Shettima ya bayyana tsaffin shugabanin kasar biyu a matsayin wadanda mutane ke samun kwarin gwiwa daga garesu kuma gwamnatin Bola Tibubu mai jiran gado za ta amfana da kwarewarsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa tsaffin shugabannin biyu suna da abubuwa da dama da al'umma za su amfana da shi da ma kasa bai daya, musamman a kan batutuwan da suka shafi kasa.
Bayanan baya-baya dangane da Kashim Shettima, Bola Tinubu, APC, Ibrahim Badamasi Babangida, Abdulsalami Abubakar, Shugabancin Kasa
Wani sashi na jawabinsa ya ce:
"Masu ruwa da tsaki alama ne na karfafa gwiwa kuma za mu cigaba da amfana da kwarewarsu. Suna da gudunmawa da dama ga kasa da al'umma baki daya. Za mu cigaba da tuntubarsu saboda shawarwari, da mahangarsu kan batutuwa da kasar ke fuskanta."
Game abin da jihar Neja za ta yi tsammani a gwamnati mai zuwa a matakin tarayya, Sanata Shettima ya tabbatar wa yan Neja sabon salon rayuwa yana mai cewa "babu wani abin damuwa domin za a magance kalubalen jihar yadda ya kamata."
Zababben mataimakin shugaban kasar, amma, bai bada cikakken bayani dangane da abin da ya da tattauna da tsaffin shugaban kasar ba.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng