PDP Ta Janye Dakatarwa Da Ta Yi Wa Shema, Fayose, Da Wasu Kusoshinta 3 Bayan Tafiyar Ayu

PDP Ta Janye Dakatarwa Da Ta Yi Wa Shema, Fayose, Da Wasu Kusoshinta 3 Bayan Tafiyar Ayu

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta soke dakatarwar da ta yi wa wasu manyan mambobinta a baya-bayan nan a cewar sakataren watsa labarai na kasa, Debo Ologunagba
  • Wadanda aka soke dakatarwarsu sun hada da tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shema, tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, Sanata Pius Anyim da wasu
  • Babban jam'iyyar hamayyar kuma ta soke tura Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue kwamitin ladabtarwa na kasa kan zargin yi wa jam'iyya zagon kasa

FCT, Abuja - Kwamitin Gudanarwa Na Kasa, NWC, na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a ranar Alhamis, ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu jiga-jiganta, rahoton The Punch.

Mambobin da aka soke dakatarwarsu sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim; Farfesa Dennis Ityavyar, Dakta Aslam Aliyu da Ibrahim Shema.

Kara karanta wannan

Mota Ɗauke da Fursunoni Ta Haddasa Babban Tashin Hankali a Babban Birnin Jiha

Fayose da Anyim
PDP Ta Janye Dakatarwa Da Ta Yi Wa Shema, Fayose, Da Wasu Kusoshinta 3. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na cikin wata sanarwar ne mai dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunaba.

An janye dakatarwa da aka yi wa jiga-jigan na PDP don hadin kan jam'iyya - Ologunaba

Ya ce an dauki matakin hakan ne yayin taron na NWC a ranar Alhamis inda mamabobin jam'iyyar suka yi tattaunawa mai zurfi kan abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar a baya-bayan nan.

Wani sashi na sanarwar:

"Wannan matakin bai shafi ikon NWC na daukar matakin ladabtarwa a kan duk wani dan jam'iyya ba a kowanne lokaci bisa tsarin kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP (kamar yadda aka gyara a 2017).
"NWC ta bukaci dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da yan jam'iyya su rika amfani da kudin tsarin mulkin PDP (kamar yadda aka gyara a 2017) da kuma sabon bukatar hadin kai da sulhu a jam'iyyar mu a wannan lokacin mai muhimmanci.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Za Ta Titsiye Sanata Da Wani Dan Majalisar Wakilai Daga Jihar Gombe Bisa Zargin Cin Dunduniyar Jam'iyya

"Ya zama dole PDP ta mayar da hankali a yayin da muke daukan duk matakin da ya dace don kwato nasarar da yan Najeriya suka ba wa jam'iyyarmu da dan takarar shugaban kasarmu, Atiku Abubakar, a zaben ranar Asabar 25 da watan Fabrairun 2023 a kotun zabe."

NWC din ta kuma kara da cewa yana da muhimmanci a yi sulhu a tsakanin shugabannin jam'iyyar domin amfaninsu da yan Najeriya.

An soke tura Ortom kwamitin ladabtarwa na kasa

Hakazalika, NWC din ta soke mika gwamnan Benue, Samuel Ortom da ta yi ga kwamitin ladabtarwa na kasa.

Gwamna Ortom ya shirya yafe takara saboda a kayar da Atiku

A wani rahoton a baya kun ji cewa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce ya shirya yafe takara don ganin Peter Obi ya zama shugaban kasa.

Ortom, wanda ke neman sanata na yankin Benue ta Arewa maso Yamma a majalisar dattijai ya ce yana iya hakura da takararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164