Zaben gwamnan 2023: Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf Gida-Gida
An kammala zaben gwamnonin Najeriya 28 yanzu illa jihar Kebbi da Adamawa da ba'a karashe zabukan ba saboda wani rikice-rikice da suka haddasa soke wasu rumfuna.
A jihar Kebbi, jam'iyyar APC na kan gaba yayinda a jihar Adamawa kuwa PDP na kan gaba.
Hukumar INEC ta zabi ranar 15 ga watan Afrilu domin kammala wannan zabe.
Cikin jihohi 26 da aka sanar da sakamakon, yan takara biyu ne kacal suka taya abokan hamayyarsu murna.
Wanda yafi daukan hankali ciki shine na jihar Kano.
Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf
A jiya Mataimakin gwamnan jihar Kano, ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen Gwamnan jihar Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zaɓaɓɓen gwamnan Kano Abba Kabir Yusif murna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lungu da sako na kasa, harda kasashen waje, sunce Gawuna yayi abinda ya dace na "Tawakkali"
Abin ya zama wani maudu'in dake tashe a kafar sadarwa ta zamani, mutane sun shiga tofa albarkacin bakin su, ba daga tsagin masu mulki ba, ba kuma daga tsagin yar adawa ba.
Masu sharhi, da masu muƙami da sanannun mutane daga lungu da saƙon ƙasar nan, har da kasashen waje sun ɓara akan batun.
Ya bi sahun gwamnan jihar Zamfara, Matawallen Muradun
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya amince da kayan da ya sha a zaɓen gwamnan jihar.
Gwamna Matawalle ya sha kashi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Dauda Lawal Dare.
A wani saƙon murya da ya aikewa mutanen jihar, gwamna Matawalle yace da shi da magoya bayan sa sun amince da hukuncin da Allah yayi, domin duk abinda ya faru haka ya ƙaddaro.
Ya bayyana cewa lokacin da ya hau kan mulki ya tattauna da dukkanin wasu.masu ruwa da tsaki domin ganin an samo hanyoyin da za a samar da ɗauwamammen zaman lafiya a jihar.
Masu fada a ji sun tofa albarkatun bakinsu kan
Bashir Ahmad, hadimin shugaba Muhammadu Buhari kuma dan jihar Kano:
"Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya sake bayyana dattako, karamci da kuma halaccin sa, mu kuma ba za mu gaji ba, wurin yi masa addu’o’i da fatan alheri a matsayinsa na jagoran mu!".
Engr. Abdullahi Garba Ramat, Shugaban ƙaramar hukumar Ungogo cewa yayi:
"Ina mai amfani da wannan dama, wannan rana, wannan lokaci in taya Engr Abba Kabir Yusif murna lashe zaben Gobnan Jahar kano, Allah ya tayashi riko, ya bashi ikon sauke wannan nauyi.
Ina mai taya jagora kwankwaso murnar samun wannan Nasara".
Kwararren lauyan nan Abba Hikima shima ya tofa albarkacin bakinsa inda yace:
"Dukkan tsoro ya kau. Kace-nacen siyasa ya kare.
Yanzu kuma sai shirin bautawa al’ummar Kano
Allah ya rika AKY,"
Ya kara da cewa:
"Shima Dr Nasiru Yusuf Gawuna yayi abunda ya dace.
Tarihi zai masa adalci."
Ayi abu a kurarren lokaci, yafi ace kwata -kwata ba'a yi ba".
Engr Muaz Magaji mai tafiyar WIN-WIN cewa yayi
"In Sha Allah
Tawakalin shine Mafi Alheri".
Rabi'u Biyora mai fafutuka, ya nisa ya sanya hoto gamida faɗin:
"Allah yayi muku jagoranci...."
Ahmad Prince Gandujiyya mai Prince 24 cewa yayi:
"Shekara hudu Kamar Yau ce.. shi Abba dai Allah Yabashi Ikon sauke Nauyi".
Kabir Dakata ya nisa gamida cewa:
"Babu shakka Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi abun a yaba masa. Allah Ya kawo masa babban rabo."
Ba'a bar mutanen Germany ba a baya, domin Baxallah Germany Sarkin Bai cewa yayi:
"Allah ya taimaka maku ta inda ba ku zata ba, ya sa ku gama lafiya Mu amfani gwamnatin fiye da yadda muke tsammani Albarkacin annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ameen."
Abdulmajid Mudassir, masani a fagen siyasa cewa yayi:
"Har na goge coat ɗi ta. Na siyo sabuwar wig (hular lauyoyi)."
Ibrahim Adam yace:
"Saida Ya Gama Zagaye Abuja Yaga Babu Sarki Sai Allah Sannan Ya Karbi Kaddara."
"Kayi abinda ya dace.Allah ya kawo babban rabo Dattijon arziki, mutumin kirki Dr. Gawuna".
Mafi yawa daga cikin wadanda suka topa albarkacin bakin su, sun yabi Dr Nasiru Yusuf Gawuna abisa ɗaukar ƙaddara da yayi na shan kaye har ya fito ya taya Abba Kabir Yusif murna.
Abin jira dai a gani shine, shin mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Murtala Suke Garo zasu fito su taya Abba Kabir Yusif murna kamar yadda Gawuna yayi.
Lokaci ne kawai alƙali.
Asali: Legit.ng