Bola Tinubu: Manyan Matsaloli Da Ke Zagaye Da Zababben Shugaban Kasa A Yayin Da Ya Cika Shekara 71
- Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, yana murnar cika shekara 71 yau, 29 ga watan Maris, duk da cece-kuce kan shekarunsa
- Kafin zamansa zababben shugaban kasar Najeriya, masu sukarsa sun tado batutuwa da dama game da shi, da dama cikinsu ba a gabatar da hujja ba
- Wasu batutuwan da ake cece-kuce kansu dangane da shi sun hada da zargin alaka da miyagun kwayoyi, wacce ba a taba gabatarwa a kotun Najeriya ba
Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, ya cika shekara 71 a yayin da ya ke murna a ranar Laraba 29 ga watan Maris.
A yayin da wasu shugabannin kasashe da fitattun mutane a Najeriya ke taya jigon na siyasan murna, yana da muhimmanci a yi rubutu dangane da manyan batutuwa game da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga dai wasu batutuwan kamar haka:
Shekara
Shekarun Tinubu na daya daga cikin abin da aka ti mahawara a kai a kansa. Wasu da dama suna ganin cewa ya fi shekarunsa na yanzu, yayin da wasu sau da yawa sun tafi shafinsa na Wikepedia suna canja labarai.
Tinubu a yau yana cika shekara 71 a duniya, ranar 29 ga watan Maris, a hukumance, amma cikin masu suka sun ce ya fi hakan tsufa.
Daya cikin irin wannan wallafar shine wanda 'Foundation of Investigative Journalism' ta yi inda ta ce shekarun zababben shugaban kasar ya kai 78.
Makaranta/Satifiket
Daya daga cikin batutuwan da ake cece-kuce a ka game da Tinubu shine makarantun da ya yi da satifiket din da ya ke da shi.
A hukumance, zababben shugaban kasar ya yi karatu a St John Primary School a Legas da Children's Home a Ibadan.
Ya yi karatun sakandare a Richard J Daley College a Chicago, Illinois, USA sannan ya yi jami'arsa a Chicago State University, Illinois, USA.
Ainihin Suna
Cikin masu sukar Tinubu akwai wadanda ke ganin ba ainihin sunansa ba kenan kuma ba daga iyalan Tinubu ya ke ba kamar yadda ya yi ikirari.
Amma, iyalinsa sun fito sun karyata hakan suna mai cewa sunansa Bola Ahmed Adekunle Tinubu.
Zargin harkalla da miyagun kwayoyi
Babban abin da ya fi janyo cece-kuce game da Tinubu shine batun alakarsa da miyagun kwayoyi.
Amma, masu zarginsa kawo yanzu ba su riga sun kallubalance sa a kotu don tabbatar da zarginsu ba sai dai tattauna abin a kafafen watsa labarai, wanda ana ganin hakan wani yunkuri ne na kawo cikas ga siyasarsa.
Obi da Obasanjo sun hadu a filin tashin jirage na Anambra, sun tattauna
A bangare guda, kun samu rahoton cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP a zaben watan Fabrairu, ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a filin tashin jirage na Awka, a jihar Anambra.
Asali: Legit.ng