Zababben Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar Takardar Shaidar Cin Zabensa, Hoto Ya Bayyana

Zababben Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar Takardar Shaidar Cin Zabensa, Hoto Ya Bayyana

  • A yau Laraba, 29 ga watan Maris ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta za ta baiwa zababben gwamnan Kano takardar shaidar cin zabe
  • Tuni zababben Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran masu ruwa da tsaki suka isa wajen taron
  • APC dai tana kalubalantar ayyana Abba a matsayin zababben gwamna cewa kamata ya yi a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba

Kano - Komai ya kankama domin mika takardar shaidar cin zabe ga zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP).

Wajen taron mikawa zababben gwamnan Kano takardar shaidar cin zabe
Zababben Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar Takardar Shaidar Cin Zabensa, Hotuna Sun Bayyana Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yusuf ya doke Nasir Gawuna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

APC ta kalubalanci sakamakon zaben gwamnan na Kano

Jam'iyyar APC ta shigar da kara sannan ta ba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)wa'adin kwanaki bakwai don sake duba sakamakon zaben da kuma ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba.

Kara karanta wannan

INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gawuna dai ya ce lallai akwai dorewar kai sosai yadda hukumar INEC ta ayyana zaben yan majalisar jihar Kano a matsayin ba kammalalle ba amma kuma ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamna.

Wannan wa'adi da jam'iyyar mai mulki ta baiwa hukumar zaben ya kare ne a ranar Talata.

Legit.ng ta nemi jin ta bakin wasu mazauna Kano don jin yadda suke jin zababben gwamnansu, Abba Gida-gida.

Zainab Ummi ta ce:

“Babu abun da za mu ce sai Alhamdulillah. Muna kyautata zaton samun shugabanci nagari daga bangaren Abba kuma muna sa ran zai daura daga nagartaccen shugabanci irin na ubangidansa Rabiu Kwankwaso.
“Kano na bukatar gyara sosai, yanzu ki duba yadda gwamnati mai ci ta giggina shaguna har a kan hanya, ta kai har a makabarta ake gine-gine wanda duk basa bisa tsari.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: “Makiyan Najeriya Ne Masu Neman a Tunbuke Shugaban INEC” – Dan Majalisa

A nashi bangaren Ahmed Sallari ya ce:

“Mu dai bamu da abun cewa sai godiya. Za ta sauya zani a Kano. Sai dai fa Gawuna ya yi abun da ya burge ni wato taya Abbanmu murna da ya yi. Muna fatan Allah ya taya shi rikon gwamnatin, Allah yasa ya zamo mafificin alkhairi garemu mutanen Kano da ma Najeriya baki daya.”

INEC ta yi kuskuren ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan Kano, Masu lura da zabe

A wani labarin kuma, masu lura da al’amuran zabe na cikin gida a jihar Kano sun yi adawa da ayyana Abba Kabir a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

Har ila yau, masu sanya idanu kan zaben sun kuma bukaci hukumar INEC da ta sake nazarin sakamakon zaben tare da yin zaben cike gurbi a wuraren da aka soke kuri’u fiye da 270,000 a jihar don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Uba Sani: ‘Dan Takaran Gwamnan Kaduna Zai Kai Jam’iyyar PDP Kotu Duk da Ya Ci Zabe

Kungiyoyin sanya idon karkashin Friday Maduka a matsayin shugaba da Alhaji Ali Abacha a matsayin sakatare ne suka bayyana hakan ranar Alhamis, 22 ga watan Maris a Kano.

Sun kuma yi watsi da rikicin da ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar da INEC ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng