Shugaban Majalisar Dattawa: Orji Kalu Ya ce Zai Janye Idan Tinubu Ya Bukaci Haka
- Bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Kalu, ya gana da Shugaba Buhari don sanar da shi ra'ayinsa na son zama shugaban majalisar dattawa
- Sai dai Kalu ya magantu cewa shugaban kasar bai ba da amsa ba kawai dai ya nuna yanayi na rashin tabbass
- Tsohon gwamnan na jihar Abia ya nuna karfin gwiwar cewa zai samu kujerar amma zai ajiye kudirinsa idan zababben shugaban kasa Tinubu ya bukaci ya yi hakan
Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu ya nuna cewa a shirye yake ya janye daga tseren neman shugabancin majalisar dokokin tarayya ta 10 idan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya nemi ya janye.
Bulaliyar majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 28 ga watan Maris, yayin zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari jan kudirinsa na son zama shugaban majalisar dattawa, Channels TV ta rahoto.
Abun da Shugaba Buhari ya ce game da kudirin neman shugabancin majalisana - Kalu
Sanata Kalu ya ce ya sanar da Shugaba Buhari aniyarsa na son zama shugaban majalisar dattawa na gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, ya ce shugaban kasar bai amsa ba kuma ya kasance cikin yanayi da ba za ka iya cewa ga abun da ke zuciyarsa ba, yana mai cewa su biyun sun dara ne a kan batun.
Tsohon gwamnan na jihar Abia ya kuma bayyana cewa bai samu tabbaci da kowa ba amma a matsayinsa na dan jam'iyya, yana kyautata zato.
Sanata Kalu ya riki cewa zai zamo mafita ga laluben da kudu maso gabas ke yi na neman kujerar shugaban majalisar dattawa.
Duk da haka, dan majalisar ya yarda cewa manyan da ke cikinsu za su iya dakatar da shi.
Yan Najeriya sun yi martani
Daleehat Suleiman Bente ya yi martani a Facebook:
"Babu wanda ya cancanci wannan matsayi da ake magana a kai sama da Uzor Orji Kalu."
Precious Lawson ya ce:
"Wannan na fada maku cewa majalisar dattawan Najeriya da majalisun dokokin Najeriya basu da yanci. Saboda haka, kada ku yi tsammanin ganin daidai. Suna yin "eh yallabai" ne ga bangaren zartarwa. wannan kuskure ne! Allah ya kyauta!!"
Ina sa ran Tinubu zai ba ni minista, Gudaji Kazaure
A wani labarin kuma, dan majalisa mai wakiltan Roni, Gwiwa, Yankwashi na jihar Jigawa, Hon Gudaji Kazaure ya bayyana cewa yana sa ran zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai ba shi mukamin minista ko wani babban kwamiti.
Asali: Legit.ng