Ka Jawo Wike Cikin Gwamnatinka, Akwai Gudummuwar da Zai Bayar, Umahi Ga Tinubu

Ka Jawo Wike Cikin Gwamnatinka, Akwai Gudummuwar da Zai Bayar, Umahi Ga Tinubu

  • Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya nemi Tinubu ya sanya Wike a gwamnatinsa domin zai yi amfani
  • Umahi, ya ce a yanzun babu zancen jam'iyya amma ba zai yuwu a rufe babin zaben 2023 ba tare da an ambaci sunan Wike ba
  • Ya ce duk wani ɗan siyasa da ke ganin zai iya cin Ribas ba tare da amincewar Wike ba mafarki yake

Rivers - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bukaci shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya jawo gwamna Wike cikin sabuwar gwamnatinsa da zai kafa.

Gwamnan Umahi ya ce takwaransa na Ribas na da tulin gudummuwar da zai baiwa Tinubu, wanda ya ci zaɓe karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki.

Gwamna Wike da Umahi.
Wike tare da gwamna Umahi Hoto: thecable
Asali: UGC

Umahi ya yi wannan furucin ne a wurin taron da Wike, mamban jam'iyyar PDP ya shirya a ƙaramar hukumar Obio-Akpor, jihar Ribas, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Dakatar da Shugaban PDP

Gwamnan Ebonyi ya ce babu ta hanyar da zaka ba da labarin babban zaɓen 2023 daga farko har ka dire ƙatshe ba tare da ka ambaci sunan Gwamna Wike ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Channels ta rahoto Umahi na cewa:

"Ina ƙara gode wa Allah mai girma wanda ya baiwa Bola Tinubu da Shettima nasara, ka duba kudirar Allah, Tinubu da Shettima sun nuna jajircewa matuƙa.
"Kai tsaye ko ta bayan fage Allah ya kawo gwamna Wike, domin ba bu ta yadda zaka gama tsokaci kan nasarar da aka samu a zabe ba tare da ka ambaci Wike ba."
"Zamu roki Asiwaju da Shettima su jawo Wike su sanya shi a cikin gwamnatin tarayya da zasu kafa nan gaba, yana da gudummuwar da zai bayar da yawan gaske."
"Zai ba da gudummuwa wajen haɗa kan kasa, ba zancen jam'iyya yanzu, haɗin kan kasa ne a gaba, ya za'a ciyar da ƙasar nan gaba kuma a haɗa kan al'ummar cikinta."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hadimin Gwamnan Arewa, Bayanai Sun Fito

Bugu da ƙari, Umahi ya yi ikirarin cewa duk wani ɗan siyasa da ke ganin zai samu asara a jihar Ribas ba tare da goyon bayan Wike ba ɗan wasan barkwanci ne.

Ina goyon bayan dakatar da Ayu - Wike

A wani labarin kuma Rikici Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Dakatar da Shugaban PDP

Gwamna Wike ya ce Ayu ne sanadin kifewar jam'iyar PDP a babban zaben da ya kammala, don haka yana goyon bayan matakin da aka ɗauka kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262