Bamu da shirin tunbuke gwamna Ikpeazu Daga Kujerarsa, Majalisar Dokokin Abiya
- Mambobin majalisar dokokin jihar Abiya sun musanta rahoton da ke ikirarin sun fara shirin tsige gwamna Okezie Ikpeazu
- Tawagar yan majalisun karkashin mataimakin kakaki, sun gana da gwamna a gidan gwamnatinsa da ke Ummuahia
- Shugaban masu rinjaye na majalisar ya ce ba bu ta yadda za'a tsige gwamna ba tare da ya samu masaniya ba
Abia - Majalisar dokokin jihar Abiya ta ce babu wani shiri a kasa na tsige gwamna Okezie Ikpeazu daga kan kujerarsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan mambobin majalisar dokokin karkashin jagorancin mataimakin kakaki, Ifeanyi Uchendu, sun gana da gwamna a gidan gwamnati, sun ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa.
Tawagar yan majalisun ta ce raɗe-raɗin da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa majalisa ta fara shirin raba Ikpeazu da kujerar gwamna ba gaskiya bane.
Da su ke kara karfafa maganar abokan aikinsu, shugaban masu rinjaye na majalisar, Solomon Akpulonu, da shugaban marasa rinjaye, Chukwu Chijioke, sun yi fatali da batun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun ayyana jita-jitar da wani shaci faɗi da gurbataccen tunanin waɗanda suka kirkiri labarin da yaɗa shi, wanda ba bu kanshin gaskiya a cikinsa.
A cewar manyan jiga-jigan majalisar biyu, gwamna Ikpeazu ya yi abinda mutane ke buƙata a jihar Abiya kuma majalisa na ɗasawa da shi, saboda haka babu bukatar tunɓuke shi.
Sun ƙara da cewa waɗanda suka ɗauki nauyin yaɗa-yaɗa jita-jitar, sun yi haka ne domin haddasa ruɗani a majalisar dokoki, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Shugaban masu rinjaye, Chukwu Chijioke, ya ja hankali na musamman cewa ba bu ta yadda za'a kulla shirin tsige gwamna ba tare da ya sani ba.
Daga nan mambobin majalisar dokokin Abiya su 13 suka roki mazauna jihar da su yi watsi da wannan jita-jita yayin da suka jaddada cewa zasu ci gaba goyon bayan gwamna Ikpeazu domin ya ƙarisa zangon mulkinsa cikin nasara.
Gwamna Ya Aike Da Sakon Ta'aziyya Mai Ratsa Zuciya Kan Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar
INEC ta mun daidai - Aishatu Binani
A wani labarin kuma Sanata Aishatu Binani Ta Maida Martani Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Adamawa
Yar takarar gwamnan jihar Adamawa karkashin inuwar APC, Sanata Aishatu Binani, ta nemi INEC ta yi abu ɗaya game da sakamakon zaben jihar.
Asali: Legit.ng