Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Kan Soke Takarar Tinubu Da Shettima

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Kan Soke Takarar Tinubu Da Shettima

  • Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake samun nasara a kotun koli ranar Juma'a, 24 ga watan Maris
  • Jam'iyyar PDP ce ta shigar kara ta na neman kotun da ta soke takarar Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ta na ikirarin cewa ba a bi ka'ida ba
  • Sai dai, kotun ta kori karar bisa rashin gamsassun hujjoji tare da cin tarar PDP Naira miliyan 5

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara a Abuja ta kori karar da jam'iyyar PDP ta shigar ta na rokon a soke takarar zababben kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima daga fafatawa a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu.

Da ta ke zartar da hukunci ta hannun mai shari'a Danlami Senchi ranar Juma'a, 24 ga watan Maris, kotun daukaka karar ta kori karar bisa rashin hujja, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Atiku Ya Yi Magana Kan Janye Kararsa Na Kallubalantar Nasarar Bola Tinubu

Asiwaju
Asiwaju Bola Tinubu ya sake nasara a kotu yayin da aka yi watsi da karar da Tinubu ta shigar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai shari'a Senchi ya ayyana ma su karar, jam'iyyar PDP, a matsayin ma su son kai, ya na mai cewa ba za ayi amfani da kotu wajen sabawa doka ba.

Ya ce PDP ta gaza ne ta na damar yin haka a doka.

Shugabancin kasa 2023: akan me aka shigar da karar?

Jam'iyyar PDP, wanda dan takararta, Atiku Abubakar, ya yi na biyu a zaben shugaban kasa ta bayyana cewa dan takarar APC, Tinubu, wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, ba shi da damar shiga zabe a dokance.

Jam'iyyar PDP ta shaidawa kotu cewa hanyar da APC da Tinubu su ka bi don nada Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, ya saba da dokar zabe, ta 2022, da aka sabunta.

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

Ta yi ikirarin cewa an tsayar da Shettima takara biyu, matsayin mataimakin shugaban kasa, da kuma takarar sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, lamarin da ta ce ya saba da doka.

Jam'iyyar PDP ta yi rashin nasara a babbar kotun tarayya da ke Abuja kafin ta daukaka kara zuwa kotun daukaka karar. Ta shigar da INEC da jam'iyyar APC a matsayin wanda ake kara.

Yadda APC ta kare kanta daga karar da PDP ta shigar

Legit.ng ta ruwaito cewa Tinubu da Shettima, ta hannun lauyoyinsu sun kalubalanci sahihancin karar tare da rokon kotun da ta yi watsi da karar.

Sun bayyana cewa PDP ba ta fahimci dalilin shigar da karar akan su ba.

A cewarsu, ba wani sashen doka da ya bawa jam'iyyar PDP, damar shiga al'amuran cikin gida na wata jam'iyya, musamman abin da ya shafi nada yan takararta a zabe.

Babbar kotun tarayya ta yi la'akari da hujjojin Tinubu da Shettima tare da watsi da karar bisa rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164