Mun Ci Zabe Ba Tare Da Peter Obi Ba, Zababben Gwamnan Abia, Alex Otti
- Mr Alex Otti, zababben gwamnan jihar Abia karkashin jam'iyyar Labour ya ce ba Peter Obi, ne sanadin cin zabensa ba
- Otti, ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis a shirin Politics Today
- Zababben gwamnan ya ce tun kafin dan takarar shugaban kasar na Labour a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ya shigo jam'iyyar Labour, dama sun taba cin zabe a baya
Jihar Abia - Zababben gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ce ya lashe zabe tun kafin dan takarar shugban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi, ya shigar jam'iyyarsu.
Otti ya bayyana hakan ne yayin wani zantawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A shekarar 2015 lokacin da na yi takara a jam'iyyar APGA, babu Peter Obi. Kuma muna da shi a bayanan mu cewa na ci zaben. A lokacin da muke shiga jam'iyyar Labour, Peter Obi bai shigo ba. Sai bayan kamar sati daya ya kira ni ya ce ya siya tikitin takarar shugaban kasa kuma zai shigo jam'iyyar Labour.
"Mun shirya don yin gwagwarmaya kamar yadda muka yi a 2015. Da mun samu kuri'un da muka samu a Abia amma watakila da tazarar bai kai haka ba. Shi yasa yana da kyau a gode wa Peter Obi. Ya taho Abia kimanin sau hudu don yi mana kamfe.
"Bana tunanin hakan ya mana wani amfani. Shi yasa ko a zaben farkon cikin kujeru takwas na majalisar wakilai na tarayya, mun samu shida kuma mun tura wasu murabus din dindindin.
"Zuwan Peter Obi ta yi amfani a kamfen din mu amma zan iya fada maka mun ci zabe a baya a Abia ba tare da shi ba."
Abba Kabir Yusuf Ya Fada Wa Masu Tattaki Zuwa Kano Don Taya Shi Murna Su Dakata, Ya Fada Musu Abin Da Ya Ke Bukata Daga Gare Su
Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan jihar Kano ya yi kira ga mutanen da suka tattaki don zuwa jihar Kano su taya shi murnar cin zabe su hakura su dakata.
Zababben gwamnan ya ce tattakin abu ne mai hatsari a halin yanzu duba da halin rashin tsaro da ake ciki a kasar, ya bukaci su zauna duk inda suke su masa addu'ar Allah ya masa jagoranci wurin sauke nauyin da ke kansa a matsayin zababben gwamna da ake fatan rantsarwa nan gaba.
Asali: Legit.ng