"INEC Ta Yi Kuskuren Ayyana Abba Gida-Gida Matsayin Zababben Gwamnan Kano", Masu Sa Ido Kan Zabe
- An kalubalanci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC bisa matakin da dauka a zaben gwamnan Kano
- Wata kungiyar sanya ido ta cikin gida a Kano ta ce INEC ta yi kuskuren bayyana Abba Kabiru Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben
- Ma su sanya idon, sun kuma yi Allah wadai da rikicin da ya biyo bayan sanar da sakamakon zabe
Kano - Masu sanya ido na cikin gida kan al'amuran zabe a Kano sun kalubalanci bayyana Abba Kabiru Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka kammala ranar Asabar a jihar.
Ma su sanya idon, sun kuma bukaci hukumar zaben da ta sa ke duba sakamakon tare da yin zaben cike gibi a wuraren da aka soke kuri'u da jimallarsu ya kai sama da kuma 270,000 kamar yadda dokar zabe ta tanada don cigaban zaman lafiya a jihar da Najeriya baki daya.
Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamis, 22 ga watan Maris, a Kano, kungiyoyin sanya idon karkashin jagorancin Friday Maduka a matsayin shugaba da Alhaji Ali Abacha a matsayin sakatare, ta ce:
''INEC ta yi amfani da na'urar BVAS don duba sakamakon zaben da ke ECBA a duk kananan hukumomi, idan aka yi haka za a ga duk sakamakon da NNPP da mabiyanta ke takama da shi na karya ne.
''INEC ba za ta ware wasu jihohi kadan daga cikin 36 don kawai cikawa wani ubangidan siyasa da tafiyarsa buri ba.
''Magudin ya yi yawa kuma akwai cin rai. A ina su ka samu wannan kuri'una kananan hukumomin Gwarzo, Tudun Wada, Bagwai, Dala, Fagge, da sauransu?
''INEC ta sabawa dokokinta ta hanyar sanar da wanda ya yi nasara alhali ba a kammala tattara sakamako ba. Kuma tazarar da ke tsakani wanda ta kai kusan dubu 130,000 ba ta haura yawan kuri'un da aka soke sama da 270,000 ba.
Sakamakon Zaben Gwamnonin 2023: Jerin Jihohi 4 Da INEC Bata Fadi Wadanda Suka Yi Nasara Ba Da Dalili
''Sashe na 65 na dokar zabe ya fayyace komai game da haka. Saboda haka, gaggawar sanar da sakamakon zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi a zaben gwamnan Kano na 2023 rashin adalci kuma ba ayi wa sauran jam'iyyu daidai ba''.
Ma su sanya idon sun kuma yi Allah wadai da rikicin da ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar da INEC ta yi.
Asali: Legit.ng