Ba Za Ta Saɓu Ba: PDP Ta Yi Watsi Da Nasarar APC A Zaben Gwamnan Jigawa
- Jam'iyyar PDP a jihar Jigawa ta ce ba ta amince da sakamakon zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris ba
- Dakta Aminu Abdullahi Taura, jigon PDP, kuma tsohon SSG na jihar Jigawa ya ce an samu rikici, tsorata masu zabe, lalata akwatin zabe da jefa kuri'a fiye da ka'ida a sassa daban-daban
- Dakta Taura ya ce masu ruwa da tsaki a jam'iyyar na PDP suna duba sakamakon zaben domin sanin mataki na gaba da za su dauka
Jihar Jigawa - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jigawa ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar Jigawa da aka kammala a jihar inda Mal. Umar Namadi Danmodi, rahoton Daily Trust.
Da ya ke yi wa shugabannin PDP da masu ruwa da tsaki jawabi kan zaben gwamana da na zaben yan majalisa, tsohon SSG, Dakta Aminu Abdullahi Taura, ya ce zaben na 2023 yana cikin mafi kallubale a tarihin jihar Jigawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa a karo na farko, an samu matsaloli da dama da suka hada da rikici, lalata akwatin zabe da karancin kayan zabe da gangan.
Saura, a cewar Taura sun hada da zabi fiye da ka'ida, tsorata masu zabe, rashin daukan mataki a bangaren jami'an tsaro da siyan kuri'u da suka saba dokar zabe.
Ya ce:
"Wadannan bakin abu ne a siyasar mu. An kama mambobin mu da wakilan mu, yayin zabe da bayan zabe ba tare da dalili ba kawai sai don su yan PDP ne yayin da yan APC da suka tada rikici suna nan suna yawo ba tare da an musu tambayoyi ba.
"Muna kira ga Sufeta Janar na yan sandan Jigawa su dauki mataki sannan su umurci a saki mambobin mu nan take."
Ya cigaba da cewa:
"Mun samu rahotanni daga dukkan kananan hukumomin jihar masu tada hankali. Abin bakin ciki ne jiha irin Jigawa da aka sani da zaman lafiya ya koma zauren tashin hankali da cuta neman mulki ta kowanne hali.
"Mutanen da suka aikata wannan shugabanni ne da ke ikirarin sun amfana da zabe na adalci da zaman lafiya a baya."
Dakta Taura ya ce INEC da sauran masu ruwa da tsaki sun gaza daukan matakai kan korafin da jam'iyyar ta yi kafin, yayin da bayan zabe, yana mai cewa PDP na nazarin mataki na gaba da za ta dauka.
Hakazalika, wakilin jam'iyyar PDP a zaben gwamna a karamar hukumar Taura, Malam Naziru Dalha Taura, yayin tattaunawa da Legit.ng Hausa shima ya yi zargin cewa jam'iyyar APC mai mulki ta tafka magudi a yankin da ya sa ido kan zabe.
A cewarsa:
"Sunyi magudi mana, ai ba su ci zabe na halal ba, bayan amfani da tada hayaniya a wasu wurare musamman Jigawa Central inda suka rasa zaben sanata.
"A ragowar yankunan mun kuma ga yadda aka ringa amfani da ma'aikatan zaben da ma jami'an tsaro wajen dangwale kuri'u. Ni da kaina a wasu mazabu da muka keyawa na ga yadda ake karbar kuri'ar jama'a, ajent na APC yana dangawalawa yana sakawa a akwati, da za a tantance da 'forensic' za a gano mutum daya ya dangwala."
Ya karkare da cewa ba zabe ne na gaskiya suka ci, zabe ne na magudi, zabe ne a kwace, zabe ne na harambe, kuma idan har za a yi bincike za a gano jam'iyyar APC ba ta da wannan kuri'un da ta samu, aringizo ne kawai aka yi.
Gwamnan Ortom Ya Fadi Zaben Sanata, Dan Takarar APC Ya Yi Nasara
A wani rahoton kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya gamu da rashin nasara a zaben sanata na mazabar Binuwai ta Arewa Yamma da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu inda dan takarar APC, Titus Zam ya ci zaben.
Asali: Legit.ng