Gwamna Umahi Ya Nada Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka
- Saura watanni 2 da yan kwanaki wa'adin mulkinsa ya kare, gwamna Umahi ya naɗa sabbin hadimai 30
- Gwamnan jihar Ebonyi ya naɗa mutanen ne domin su rika bibiyar ayyukan da gwamnati take gudanarwa a faɗin jihar
- Ya bukaci hadiman su zage dantse su yi amfani da wannan lokacin wajen kara gogewa a sha'anin mulki
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Davud Umahi, ya naɗa sabbin hadimai 30 domin su ƙara karfafa shugabanci mai kyau ga mazauna jihar yayin da ya rage watanni 2 ya sauka.
Jaridar PM News ta rahoto cewa yayin rantsar da mutanen a Abakaliki ranar Laraba, gwanna Umahi ya umarci sabbin hadiman su maida hankali wajen aiki tun a matakin farko.
Ya roki mutanen da ya naɗa da su yi aiki a kananan hukumomin jihar domin tabbatar da romon Demokaradiyya ya isa ga talakawa ba tare da nuna wariya ba.
Ya yi bayanin cewa ya zakulo su kuma ya naɗasu waɗannan mukaman ne bayan la'akari da gudummuwar da suka bayar lokacin suna matsayin Ko'idinetoci a kananan hukumomi daban-daban.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Wasu daga cikin manyan ayyukan da muke su ku sa wa ido sun haɗa da, Jirgin sama, faɗaɗa Titin Ring-Road, Fenti da kwalliya, da kuma filin wasan kwallo da aikin gina gadojin sama."
"A koda yaushe ku riƙa aiki da kwanishinan ayyuka, Sufuri da gidaje wajen sauke nauyin da muka ɗora muku."
Gwanna Umahi ya buƙaci hadiman su yi amfani da ragowar watanni biyu da suka rage su ƙara samun gogewar aiki domin ci gaban jihar Ebonyi.
Jerin sunayen sabbin hadimai 30
Legit.ng Hausa ta tattaro muku sunayen mutane 30 da gwamna Umahi na APC ya naɗa a matsayin hadimai, ga su kamar haka;
Sun Ki Allah Ya Nufa: Yadda Na Kusa Da Ni Suka Ci Amanata a Lokacin Zabe, Gwamnan APC Yayi Bayani Mai Sosa Rai
1. Augustina Nwaovu
2. Obinna Nwaiboko
3. Baron Anya
4. Innocent Eluu
5. Chima Okoro Eze
6. Victor Nwaobasi
7. Elias Igwe
8. Ikechukwu Nwafor
9. Kingsley Akam
10. Theodore Iheta
11. Emmanuel Ekuma
12. Martin Oga
13. John Ogodo
14. Afulike Uchechukwu
15. Justice Agu
16. Misis Blessing Nweze
17. Victor Nwoke
18. Chijioke Nwuzor
19. Uche Nwankpuma
20. Misis Roseline Nkwuda
21. Patrick Enyi
22. Tochukwu Uzor
23. Misis Sharon Umahi
24. Ejike Agbo
25. Stephen Ogenyi
26. Arthur Ude Umanta
27. Ikechukwu Anoke
28. Uchenna Ugwuta
29. Sebastian Ojiogu
30. Ama Okoro.
PDP ta lashe zaben gwamna a Enugu
A wani labarin kuma INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Enugu Mai Cike da Ruɗani
Bayan kai ruwa rana, baturen zaɓe ya ayyana ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a matsayin wanda ya samu nasarar zama zaɓaɓɓen gwamna a jihar Enugu.
Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan INEC ta bayyana wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Abiya.
Asali: Legit.ng