INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamna a Jihohi 28

INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamna a Jihohi 28

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta kammala feɗe sakamakon zaben gwamna na kowace jiha daga cikin 28
  • Zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi ya gudana ne a jihohi 28 ranar Asabar ɗin da ta gabata
  • INEC ta sanar da cewa zata ci gaba da tattara sakamako a jihohi 2 da ta dakatar, watau Abiya da kuma Enugu

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta kammala bita da nazari kan sakamakon zaben gwamnoni wanda ya gudana ranar Asabar da ta gabata a jihohi 28.

A cewar INEC, ta gama nazari kan zaben gwamna a jihohin Abiya da Enugu, inda tun farko ta dakatar da tattara sakamako ɓiyo bayan maguɗin da aka shirya yi da rigingimin da suka faru.

Mahmud Yakubu.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: Mahmud Yakubu

Vanguard ta tattaro cewa kwamishinan INEC na ƙasa mai kula da sashin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a, Festus Okoye, ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu

INEC ta tunatar da zaman da ta yi ranar Litinin 20 ga watan Maris, 2023 kuma ta duba sakamakon zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ɗaya bayan ɗaya, ta yi nazari a kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba a ranar 18 ga watan Maris, 2023, INEC ta gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya bayan samun tsaiko, wanda ya kai har ta ɗage zaɓen da mako ɗaya.

The Nation ta rahoton Okoye na cewa:

"A wurin taron, INEC ta yanke shawarin dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a wasu sassan jihohin Abiya da Enugu, domin ta samu damar nazari kan sakamakon dukkan jihohi."
"A halin yanzu hukumar ta kammala bitar sakamakon baki ɗaya, kuma za'a ci gaba da tattara sakamakon zabe a Abiya da Enugu yau 22 ga watan Maris, 2023."
"INEC ta yaba da yadda mutanen waɗan nan jihohi biyu suka yi hakuri kuma suka fahimci matakin da ta ɗauka, zamu ƙarisa tattara sakamako kamar yadda aka fara."

Kara karanta wannan

“Ku Gaggauta Sakin Sakamakon Abia da Enugu”, Peter Obi Ga Hukumar INEC

INEC Ta Fitar da Sakamakon Zaben Yan Majalisun Jihar Edo

A wani labarin kuma Hukumar Zabe Ta bayyana sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin jihar Edo kwana uku bayan kammala jefa kuri'a.

A wata sanarwa da mai magana da yawun INEC na jihar ya fitar, ya nuna PDP ce a kan gaba wajen samun yan majalisu mafi yawa.

Haka nan INEC ta ayyana sakamakon zaben yan majalisu na mazaɓu uku da ba su kammalu ba watau 'Inconclisive' kamar yadda kalmar ta shahara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262