“Ku Sanar Da Sakamakon Zaben Abia Da Enugu Ba Tare Da Bata Lokaci Ba”, Obi Ga INEC

“Ku Sanar Da Sakamakon Zaben Abia Da Enugu Ba Tare Da Bata Lokaci Ba”, Obi Ga INEC

  • Shugabancin jam'iyyar Labour Party na kasa bai ji dadin dakatar da sakamakon zaben jihohin Abia da Enugu ba
  • A wata sabuwar sanarwa, dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi ya umurci INEC da ta gaggauta sanar da sakamakon zaben jihohin biyu
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya jaddada cewar jinkirta sakamakon zaben jihohin zai shafi sahihancin hukumar

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya nuna rashin jin dadinsa kan abun da ya bayyana da ci gaba da jinkiri wajen sakin sakamakon zaben gwamnonin Abia da Enugu.

A cikin wata sanarwa dake da sa hannunsa a ranar Talata, 21 ga watan Maris, Obi ya bukaci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta gaggauta sakin sakamakon.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben Gwamnonin 2023: Jerin Jihohi 4 Da INEC Bata Fadi Wadanda Suka Yi Nasara Ba Da Dalili

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi
“Ku Sanar Da Sakamakon Zaben Abia Da Enugu Ba Tare Da Bata Lokaci Ba”, Obi Ga INEC Hoto: Mr Peter Obi
Asali: Twitter

Obi ya yi martani kan dakatar da sakamakon zaben Abia da Enugu

Legit.ng ta rahoto a baya cewa INEC ta dakatar da shirin tattara sakamakon zabe a Abia saboda farmakin da aka kai daga cikin ofishoshinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Obi ya ce ci gaba da jinkiri wajen sanar da sakamakon zai kawo tsaiko ga aniyar hukumar da sahihancinta.

Obi ya baiwa INEC babban aiki

Obi ya bukaci hukumar da ta gaggauta yin nazari da yayyafawa halin fargabar da ake ciki a Najeriya musamman ma a wadannan jihohin biyu ruwan sanyi, rahoton Sahara Reporters.

Gwamnatin Matawalle ta saka dokar hana fita a Zamafara

A wani labari na daban, mun ji cewa bayan ayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Zamfara wanda ya ba dan takarar jam'iyyar PDP, Dauda Lawal Dare nasara, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Hana Fita Daga Wayewar Gari Zuwa Dare

Gwamnatin Bello Matawalle ta ce ta sanya dokar ne domin kwantar da kurar da ya tashi a jihar wanda ya kai ga lalata kayan gwamnati, fashe-fashen shaguna da sauransu duk da sunan murnar faduwar gwamnati mai ci a zaben.

Rahoton ya kuma ce tuni gwamnati ta ba hukumomin tsaro umurnin tabbatar da bin dokar domin gudun barkewar rikici da tashin hankali a jihar, kuma ta ce duk wanda aka samu ya karya dokar zai gamu da fushin hukuma da doka a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng