Yanzu Yanzu: An Sanya Dokar Hana Fita Daga Wayewar Gari Zuwa Dare a Zamfara
- Gwamnatin Bello Matawalle na jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita a jihar saboda tabbatar da doka da oda
- Bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan 2023 a jihar wanda Lawal Dare na PDP ya yi nasara, gwamnatin jihar ta ce akwai bukatar sanya dokar kulle a jihar
- Kwamishinan labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ce wasu mutane sun lalata kayan gwamnati da dukiyoyin jama'a da sunan murnar cin zabe
Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita bayan sanar da sakamakon zaben gwamna a fadin jihar, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Gwamna Bello Matawalle ya sha kaye a kokarinsa na son zarcewa a kan kujerarsa yayin da Dauda Lawal Dare na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya lashe zaben.
A wata sanarwa da Ibrahim Dosara, kwamishinan labarai na jihar ya saki, ya ce an dauki matakin ne saboda tashin hankali.
Channels TV ta nakalto Dosara yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Cike da takaici, gwamnatin jihar Zamfara ta lura da barna da lalata kayan gwamnati da dukiyoyin jama’a da aka yi inda ake jiwa wasu mutane da ba su ji ba basu gani ba raunuka daban-daban da sunan murnar bayyana sakamakon zaben gwamna a jiya.
"Rahotannin da gwamnati ta samu sun nuna cewa an yi asarar rayuka, an lalata gidaje sannan an fasa shaguna da sace-sace.
"Domin hana faruwar irin haka, gwamnatin ta ga ya wajabta ta saka dokar kulle daga 8:00 na dare zuwa 6:00 na asubahi har zuwa lokacin da zaman lafiya zai dawo. An umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin dokar."
Legit.ng Hausa ta lura cewa gwamnatin Kano ta dauki irin wannan matakin bayan sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar.
Nasir Gawuna, mataimakin gwamnan jihar wanda ya yi takara a zaben karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya sha kaye a hannun Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam’iyyar New Nigerian Peoples Party’s (NNPP).
Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ayyana dokar hana fita domin hana barkewar rikici amma wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP suka bi inda suka yi tururuwan fitowa tituna don murnar kayen da jam’iyya mai mulki ta sha.
Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin INEC a Ogun kan sakamakon zaben gwamna
A wani labarin kuma, jama'a sun gudanar da zanga-zanga inda suka mamaye ofishin hukumar zabe a jihar Ogun domin kalubalantar ayyana Dapo Abiodun na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Asali: Legit.ng