"Na Yafe Muku" Gwaman Nasarawa Ya Aike da Sako da Wadanda Ba Su Zabe Shi Ba
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya miƙa godiya ga magoya bayansa da suka fito suka sake zaɓen shi ranar Asabar
- Ya bayyana cewa wa'adin mukinsa na biyu zai ɗora daga inda ya tsaya ta yadda kowa ne ɗan jiha zai amfana babu nuna wariya
- Zababben gwamna a karo na biyu ya aike da sako ga yan adawa cewa shi na su ne kuma bai riƙe kowa a zuciya ba
Nasarawa - Zababben gwamnan jihar Nasarawa a karo na biyu, Abdullahi Sule, ya yi martanin farko bayan lashe zaɓen ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.
Da yake jawabi a gidan gwamnatinsa da ke Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa, Sule ya ce ya yafe wa dukkan waɗanda ba su kaɗa masa kuri'unsu ba a zaben da aka kammala.
A rahoton Daily Independent, Gwamna Sule ya gode wa dubbannin masu kaɗa kuri'a, waɗanda suka sadaukar da lokacinsu, suka jefa masa kuri'a don jaddada aminta da gwamnatinsa.
Ya kuma ɗauki alkawarin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da gina shugabanci na gari da kuma shayar da romon Demokuradiyya a faɗin jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar Punch ta rahoto gwamna Abdullahi Sule na cewa:
"Dukkan mutanen da suka zabe ni da ma waɗanda ba su zabe ni ba duk nawa ne. Hakurin da Allah ya fi so shi ne wanda mutum zai yafe wa ɗan uwansa duk da yana da ikon ramawa."
"Mun gode wa Allah yadda ya taimake mu zabe ya zo kuma aka gama lafiya. Duk wasu labarai na abinda ka iya faruwa, lalacewar rashin tsaro da ake ganin zai faru, sun fi damu na a cikin zuciya fiye da zaɓe."
"Saboda ba na fatan burina ya yi sanadin raunata wani ko rasa rayuwar mutum ɗaya a jihar Nasarawa."
Ya jaddada godiyarsa ga magoya baya yayin da ya nuna cewa su ne ƙashin bayan yuwuwar sake zaɓensa a karo na biyu.
Jihohin da aka samu tsaiko a zaben gwamna
A wani labarin kuma mun kawo muku jerin Jihohin da INEC Ta Ayyana Zaben Gwamna da Bai Kammalu Ba ko Ta Dakatar da Haɗa Sakamako.
An gama zabe tare da sanar da sakamako a jihohi 24, akwai wasu jihohi da aka samu tsaiko, mun haɗa maku wadannan jihohin da dalilin da yasa a ka samu jinkiri.
Asali: Legit.ng