Jerin Sunaye Sabbin Gwamnoni da Aka Zaba Zangon Farko, Jam'iyyu da Jihohinsu

Jerin Sunaye Sabbin Gwamnoni da Aka Zaba Zangon Farko, Jam'iyyu da Jihohinsu

'Yan Najeriya zasu ga sabbin fuskoki a dandamalin siyasar ƙasar nan daga ranar 29 ga watan Mayu, 2023, idan aka rantsar da waɗanda suka samu nasara.

Wannan ya biyo bayan zaben da mutane suka yi wa wasu sabbin hannu da zasu jagoranci tafiyar da harkokin shugabancii a jihohinsu a karo na farko.

Gwamnoni masu jiran gado da Allah ya ba nasara a zabukan da aka kammala sun ƙunshi na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), babbar jam'iyyar adawa PDP da NNPP mai kayan marmari.

Sabbin gwamnoni masu jiran gado
Sabbin gwamnoni uku Hoto: Uba Sani/Uno
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro muku sunayen sabbin zababbun gwamnoni da zasu hau kan madafun iko a karon farko, jam'iyyunsu da kuma jihohin da suka ci zaɓe.

Gwamnoni a inuwar APC

1. Ahmed Aliyu - Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwan Sani 5 Dangane Da Rayuwar Dauda Lawal, Sabon Gwamnan Jihar Zamfara

2. Dakta Dikko Umaru Raɗɗa - Katsina

3. Malam Uba Sani - Kaduna

4. Bassey Otu - Kuros Riba

5. Muhammed Bago - Neja

6. Francis Nwifuru - Ebonyi

7. Umar Namadi Ɗan Modi - Jigawa

Gwamnoni a inuwar PDP

1. Umo Uno - Akwa Ibom

2. Siminialayi Fubara - Ribas

3. Kefas Agbu - Taraba

4. Caleb Mutfwang - Filato

5. Sheriff Oborevwori - Delta

6. Dauda Lawal Dare - Zamfara

Gwamna 1 tal a inuwar NNPP

1. Abba Kabir Yusuf - Kano

Kawo yanzun, waɗannan gwamnonin da muka kawo muku a sama, zasu fara zangon mulkinsu na farko a jihohinsu bayan rantsar da su ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A ranar Asabar din karshen makon da ya gabata, 18 ga watan Maris, aka gudanar da zaben gwamnoni a jihoh in Najeriya 28 tare da zaben mambobin majalisar dokoki.

Legit.ng ta fahimci cewa akwai sauran jihohin da za'a iya samun sabbin fuskoki, kamar Adamawa da Kebbi, waɗanda INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

A Karon Farko a Shekara 24, PDP tayi Nasara a Zamfara, Gwamnan APC Ya Rasa Tazarce

Gwamna Ayade Ya Kori Manyan Hadimansa Biyu, Ya Nada Sabbi

A wani labarin kuma Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya sauke fushinsa kan wasu mashawarta na musamman guda biyu

A wata hira da Sakataren watsa labaran gwamnan, ya ce Ayade ya kori hadimansa guda biyu kuma ya faɗi waɗanda zasu maye gurbinsu.

Gwamna Ayade ya nemi takarar Sanata a zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 amma bai kai ga nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262