Muhimman Abubuwan Sani Dangane Da Rayuwar Dauda Lawal Sabon Gwamnan Zamfara
A abinda za a iya cewa shine babban kayen da akayi a zaɓen gwamnoni na 2023, Lawal Dauda, ma'aikacin banki, ya tiƙa gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da ƙasa.
A cewar baturen zaɓen jihar, Farfesa Kassimu Shehu, Dauda Lawal Dare na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya samu ƙuri'u 377,726 inda ya kayar da Matawalle na jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 311,976. Rahoton Daily Trust
Ga wasu muhimman abubuwan sani dangane da sabon angon jihar Zamfara:
1. Haihuwa
An haifi Dauda Lawal Dare a rana 2 ga watan Satumban 1965 a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Karatu
Lawal yayi karatun firamaren sa a ƙauyen mahaifiyar sa, Guga cikin jihar Ƙatsina. Yayi digirin sa na farko a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1987 inda ya karanci kimiyyar siyasa.
Yayi digirin sa na biyu a jami'ar Ahmadu Bello University Zaria a shekarar 1962. Yana kuma da digirin digir daga jami'ar Usmanu Dan Fodiyo dake Sokoto.
Lawal yayi kwasa-kwasai da dama a manyan makarantu da suka haɗa da London School of Economics, Harvard Business School, Oxford University Business School da Lagos Business School, da sauran su.
3. Aiki
Ya fara aiki a matsayin malamin makaranta a shekarar 1989 da hukumar Agency for Mass Mobilization for Social and Economic Reliance Nigeria. A shekarar 1989, ya koma aiki da kamfanin Westex Nigeria Limited a matsayin mataimakin manaja.
A shekarar 1994 an naɗa shi jami'in jakada sannan daga baya jami'in Chief protocol, a ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Washington D.C na ƙasar Amurka.
A shekarar 2003, ya fara aiki da ankin First Bank, inda ya riƙe muƙamai da dama.
4. Kasuwanci
Dauda Lawal ya kafa kamfanunnika da dama a jihar Zamfara domin rage rashin aikin yi a jihar.
Kamfanunnikan da ya kafa sun haɗa da Zam blocks, kamfanin bulo da babu kamar sa a jihar, Zam rice mills, Azuma water, da kamfanin taki na Zam agrochemical (kamfanin haɗa taki mafi girma a Arewacin Najeriya.)
5. Nasara kan EFCC a kotu
Lawal Dauda ya taɓa yin nasara kan hukumar hana cin hanci da rashawa (EFCC) a kotun ƙoli.
A shekarar 2021 kotun ƙoli ta umurce hukumar EFCC ta mayar da N9bn da ta ƙwace a hannun sabon gwamnan na Zamfara.
Asali: Legit.ng