APC Ta Yi Babban Rashi, PDP Ta Lashe Kujerun Yan Majalisar Jiha 25 Cikin 26 a Osun

APC Ta Yi Babban Rashi, PDP Ta Lashe Kujerun Yan Majalisar Jiha 25 Cikin 26 a Osun

  • Jam'iyyar APC ta gamu da rashin nasara mai girma a zaben mambobin majalisar dokokin jihar Osun
  • Bayan rashin nasara a zaben shugaban ƙasa, APC ta sake rasa kujerun majalisa 25 cikin 26 ga jam'iyyar PDP mai mulkin Osun
  • Karo na uku kenan da PDP ta tumurmusa APC a zabe a Osun, zaben gwamna, shugaban kasa da kuma yan majalsu

Osun - Jam'iyyar PDP ta lashe kujeru 25 cikin 26 na mambobin majalisar dokokin jihar Osun, waɗanda ke hannun jam'iyyar APC kafin yanzu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta bayyana a hukumance, jam'iyyar APC ta ci kujera ɗaya ne tal ta mazaɓar Boripe Boluwaduro.

Majalisar dokokin Osun.
Zauren majalisar dokokin jihar Osun Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yayin da shugabanni da mambobin PDP suka ɓarke da murnar samun nasara, mambobin APC da jagororinsu sun fara zargin juna kan wannan babban rashin sa'a da suka yi a zaɓe.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ta Lashe Kujeru 22 Cikin 26 Na Majalisar jiha a Ondo

Jam'iyyar PDP ta samu nasarar yin ƙasa-ƙasa da jam'iyyar APC a zabuka uku da aka gudanar a jihar Osun a 'yan baya-bayan nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da fari, PDP ta lallasa APC a zaben gwamnan jihar wanda ya gudana a watan Yuli, 2022, ta maimaita a zaben shugaban ƙasa da 'yan majalisun tarayya, na ƙarshe kuma shi ne zaben mambobin majalisar dokoki.

Me ya jawo wa APC wannan babban rashin nasara?

Da yawan masu hasashe sun alaƙanta abinda ya haddasa wa APC rashin nasara da rigingimun cikin gida da suka ƙi ci kuma suka ƙi cinyewa a jihar.

Rigimar da ake ganin ta fi yi wa APC illa ita ce wacce ke tsakanin tsohon gwamna, Adegboyega Oyetola, da kuma wanda ya gada kuma Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.

Bayanai sun nuna cewa zaben mambobin majalisar dokokin Osun da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata cike yake da rikici da rashin haɗin kan masu kaɗa kuri'a, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: PDP ta yi jana'izar APC, ta lashe kujerar majalisa ta farko a jihar APC a Arewa

NNPP ta ci majalisar Rogo

A wani labarin kuma Jam'iyyar NNPP Ta Lashe Kujerar Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano Mai Wakiltar Rogo

Baturen zaben mazaɓar ya ayyana Isma'il Falgore a matsayin wanda ya samu nasara karkashin inuwar NNPP bayan samun kuri'u mafi rinjaye.

Mista Falgore ya sha alwashin aiwatar da wakilci mai kyau da nagarta ga mutanen mazaɓar Rogo da suka miƙa masa amana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262