Jam'iyyar NNPP Ta Lashe Kujerar Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano
- Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta fara lashe kujerun mambobin majalisar dokokin jihar Kano
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana ɗan takarar NNPP a matsayin wanda ya lashe zabe a mazaɓar Rogo
- Isma'il Falgore ya gode wa mutanen Rogo bisa damar da suka ba shi, ya yi alƙawarin ba zai basu kunya ba
Kano - Ismail Falgore na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya lashe zaben mamban majalisar dokoki mai wakiltra mazabar Rogo a jihar Kano.
Baturen zaɓe a mazaɓar ya ayyana Falgore a matsayin wanda ya samu nasara bayan ya samu kuri'u 18,211, wanda suka ba shi damar lallasa Zarewa Magaji na APC, mai kuri'u 11,007.
A wata sanarwa da ya fitar bayan sanar da sakamakon, zaɓaɓɓen dan majalisar ya miƙa godiya ga mazauna Rogo bisa goyon baya da amanar da suka damƙa masa.
Falgore ya kuma ɗauki alƙawarin zai yi aiki ba kama hannun yaro domin inganta rayuwar mutanen mazaɓar baki ɗaya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ina godiya ga mutanen mazaɓar Rogo bisa wannan dama da suka bani na wakilce su a majalisar dokokin jihar Kano. Ina baku tabbacin ba zan yi wasa da goyon bayan da kuka bani ba."
"Zan yi aiki tukuru ba kama hannun yaro wajen tabbatar da mutanen mazaɓata sun samu abinda su ke buƙata," inji Falgore.
Bugu da ƙari, ya yi alƙawarin cewa zai haɗa kai da sauran mambobin majalisar dokoki wajen yin dokokin da zasu amfani rayuwar mazauna jihar Kano.
"Zan haɗa kai da sauran abokan aikina na majalisa wajen yin dokokin da zasu ƙara gyara rayuwar mazauna Kano. Ina da yakinin idan muka haɗa kai zamu ba mara ɗa kunya."
Zan Zama Gwamna Idan Yan Uwana Mata Suka Zabe Ni, Aishatu Binani
A wani labarin kuma Yar takarar gwamna a inuwar APC a jihar Adamawa ta ce zata samu nasara cikin sauki idan mata suka abu ɗaya.
Sanata Aishatu Binani ta ce a halin da ake ciki yanzu mata ke da mafi rinjayen kuri'u kuma ta samu goyon bayan da aka yi tsammani daga maza.
A cewarta tana alfahari kasancewar ta shiga fafatawar da kowa ya san maza ne suka mamaye.
Asali: Legit.ng