INEC Ta Fara Dora Sakamakon Zaben Gwamnoni da Na'urar BVAS

INEC Ta Fara Dora Sakamakon Zaben Gwamnoni da Na'urar BVAS

  • INEC ta fara ɗora sakamakon zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a Fortal ɗinta ta hanyar amfani da na'urar BVAS
  • Rashin ɗora sakamakon a zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 ya haddasa cece-kuce a faɗin Najeriya
  • Daga cikin sakamakon da aka hanga a Fotal ɗin IReV har da na rumfunan jihar Kano da ke arewa maso yamma

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ɗora wasu sakamakon zaben ranar Asabar 18 ga watan Maris a shafinta ta hanyar amfani da na'urar BVAS.

Idan baku manta ba rashin ɗora sakamakon zaɓe da BVAS a zaben shugaban kasa da aka kammala ranar 25 ga watan Fabrairu, ya haddasa kace-nace a faɗin Najeriya.

Na'urar BVAS.
INEC Ta Fara Dora Sakamakon Zaben Gwamnoni da Na'urar BVAS Hoto: INECNigeria
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa duk da INEC ta ba da uzurin samun tangardar sadarwa yayin tura sakamakon ta BVAS, da yawan masu sukar lamarin ba su gamsu da uzirin ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Wargaza Akwatunan Zabe Sama da 10

Sai dai hukumar INEC ta yi wa 'yan Najeriya alkawarin ƙara inganta amfani da na'urar a zaben da ke gudana yau Asabar na gwamnoni da yan majalisun jihohi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda aka fara dora sakamako da BVAS

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sakamakon zabe a gunduma ta 001, PU 039, ƙaramar hukumar Yenagoa, jihar Bayelsa, BVAS ta ɗora shi a Fotal ɗin INEC da misalin ƙarfe 1:58 na rana.

A zaben na majalisar dokoki, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri'u Shida yayin da jam'iyyar PDP ta tashi da kuri'u 13.

Haka zalika, INEC ta dora wasu sakamakon zabe daga rumfunan zaben jihar Kano a shafinta na musamman da ake kira IReV Fotal.

Ana amfani da na'urar BVAS wajen tantance masu kaɗa kuri'a a wurin zabe yayin da bayan kammala kirga kuri'u, na'urar zata tura sakamakon rumfar kai tsaye zuwa Fotal ɗin INEC.

Kara karanta wannan

Kash! Na'urorin tantance masu kada kuri'u guda 22 sun yi batan-dabo a wata jiha

Rikici Ya Kara Tsananta a Kano

A wani labarin kuma Rikici ya kara yaɗuwa a Kano yayin zaben gwamna, zuwa yanzu an lalata akwatuna akalla 10

Wasu rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Rimin Gado, sun nuna cewa yan daba sun farfasa akwatunan zabe, jami'an tsaro da kyar suka sha zuwa ofishin INEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262