Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Sace Akwatuna Sama da 10
- Rikici da tashin hankali sun ƙara yaɗuwa yayin da ake ci gaba da gudanar da zaben gwamna da 'yan majalisar jiha a Kano da sauran jihohin Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa akalla Akwatunan zaben 10 wasu 'yan daba suka farfasa a yankin ƙaramar hukumar Rimin Gado, tilas jami'an NSCDC suka yi takansu
- An ce wasu jami'an tsaro na hukumar Sibil Difens sun koma Ofishin INEC da raunuka kuma wujiga-wujiga ɗauke da wasu akwatunan zaɓe
Kano - Rahotanni sun bayyana cewa akalla Akwatunan zaɓe 10 aka wargaza a rumfuna daban-daban da ke yankin ƙaramar hukumar Rimin Gado, a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana cikin gudanar da zaɓe lami lafiya lokacin da wasu tsagerun 'yan daba suka ta da hayaniya kuma suka lalata akwatunan zaɓe.
Wasu jami'an hukumar tsaro ta Sibil Defens, wadanda suka koma Ofishin INEC da ke Rimin Gado ɗauke da wasu Akwatuna, sun ce sai da aka agaza musu suka tsira.
Ɗaya daga cikin jami'an NSCDC na ɗauke da raunuka a kusan ko ina a kafaɗarsa yayin da Kayan aikinsa sun yi butu-butu da ƙura.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wane rumfuna ne aka samu tashin tashina?
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa gundumomi da adadin rumfunan zaben da aka samun tashin rikici sun haɗa da; Dogurawa (Akwatuna huɗu aka lalata), Jujin Kosau, gundumar Jili, Yelwa, Kongi 009.
Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da zaben gwamna ya ɗauki zafi musamman tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da NNPP mai kayan marmari.
Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusu Gawuna, na neman APC ta ci gaba da mulki yayin da Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ke neman kwace mulki a inuwar NNPP..
Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19
A wani bangaren kuma, Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Safiyar Yau Asabar 18 ga watan Maris, 2023
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya sun yi nasarar ceto malaman zabe na wucin gadi 19 waɗanda aka yi awon gaba da su a jihar Imo, kudu maso gabas.
Asali: Legit.ng