Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Borno, Kebbi, Zamfara da Yobe
A gaban jami'an tsaro, ana sayen kuri'u a Yobe
A bainar idon jami'an tsaro, ana sayen kuri'u a Hausari Sabon Feggi, karamar hukumar Nguru. a jihar Yobe
Sanata Kashim Shettima ya kada kuri'arsa.
Mataimakin Zababben Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya kada kuri'arsa.

Source: Twitter
Gwamna Mai Mala Buni Ya kada kuri'arsa
Gwamnan jihar Yobe mai neman zarcewa, Mai Mala Buni, ya kada kuri'arsa a zaben dake gudana yau.
ChannelsTV ta ruwaito cewa Buni ya kada kuri'arsa a Bulturam Yerimaram a karamar hukumar Gujba.
Mataimakin gwamnan Borno ya kada kuri'arsa
TheCable ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar Borno, Kadafur, ya kada kuri'arsa a mazabarsa dake karamar hukumar ta jihar

Source: Twitter
Ana sayen kuri'u a Kebbi
A rumfar zaben Dan Shafarma, Koikani, karamar hukumar Argungun an ga masu sayen kuri'u kuma wakilan jam'iyyu sai sun ga abinda kowa ya zaba.
Zabe na gudana lafiya lau a Yobe
Zabe na gudana lami-lamiya a karamar hukumar Potiskum na jihar Yobe.
Kawo yanzu babu wani rahoton rikici da tashin-tashina a jihar gaba daya.
Na'uarar BVAS ta samu matsala a Kebbi
A rumfar zabe na PU 001 dake Garka Hakimi, Saransosa, karamar hukumar Maiyama dake jihar Kebbi na'urar BVAS bau daukar hotuna da ayar hannun masu zabe.
Ana jiran jama'a su zo su kada kuri'a a Yobe
Dubunnan yan gudun Hijra a Borno sun tafi kada kuri'unsu
HumAngle ta ruwaito da daruruwan yan gudun hijra suka tafi garuruwansu domin kada kuri'unsu.
Birnin Kebbi
Jami'an INEC sun dira gundumar Nasarawa, birnin Kebbi, komai na tafya dai-dai amma masu kada kuri'a basu iso ba.