Zaben Ranar Asabar: Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus Daga Awanni Kadan Kafin Zabe, Ya Bayyana Dalili
- Dele Omenogor, shugaba kuma jigon jam'iyyar, Peoples Democratic Party, PDP, a garin Amai da ke karamar hukumar Ukwuani a Jihar Delta, ya fice daga jam'iyyar
- Ficewar Omogonor na zuwa ne awanni kadan kafin gudanar da zaben gwamna da na yan majalisa a jihar
- Jigon na Peoples Democratic Party, PDP ya zargi gwamnatin Ifeanyi Okowa a jihar da nuna rashin adalci da daidaito ga al'ummar Amai
Asaba, Delta - Chief Dele Omenogor, jagoran jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a karamar hukumar Ukwuani da ke Jihar Delta, ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar.
Jigon na PDP ya bayyana irin yadda aka wofantar da masarautar Amai da gaba daya kasar Ukwuani a gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar, kusan shekara 8, kamar yadda jaridar The Tribune ta ruwaito.
Me yasa jigon PDP ya bar tsagin Okowa awannj kadan kafin zabe
An bayyana hakan ne ta wata takarda da Omegonor ya mikawa shugaban jam'iyyar PDP na mazaba ta shida Amai a karamar hukumar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Omenogor ya zargi gwamnatin Okowa da nuna rashin daidaito da da adalci ta hanyar wofantar da al'ummar Amai lokacin da ya ke ayyukan cigaba a karamar hukumar Ukwuani.
Ya bayyana cewa ya yi iya abin da zai iya yi wa jam'iyyar PDP, ta hanyar saka lafiya da dukiyarsa don karfafa jam'iyyar a Amai da Ukwuani, amma garinsa bai kurbi romon dimukradiyya ba.
Muhimman bayanai game da PDP, Dele Omenogor, Ifeanyi Okowa, Delta, zaben 2023
Wani bangaren takardar ya ce:
''Na shiga jam'iyyar PDP a shekarar 2001 saboda ina son amfani da ita don al'ummata su amfana da dimukradiyya, amma abin takaici ne bayan shekara 22, an samu kadan ko ma ba a samu hakan ba.''
Jigon na PDP ya bayyana cewa a karan kansa ya ke daukar dawainiyar jam'iyyar a mazaba ta 6, saboda son cigaban yankinsa da al'ummarsa.
"Babu Wanda Na Janye Wa Takara", Asake, Dan Takarar Gwamna Na LP A Kaduna
A wani rahoton, Jonathan Asake, dan takarar gwamna na jam'iyyar LP a Jihar Kaduna ya karyata jita-jitar cewa ya janye wa dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru, takara a zaben ranar Asabar da ta tafe.
Ya sanar da hakan ne yayin wani hira da ta yi da manema labarai a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jama'a a yayin mayar da martani kan batun.
Asali: Legit.ng