Jerin Jihohi 8 Da Ba Za a Gudanar Da Zaben Gwamna Ba Ranar Asabar
A ranar Asabar, 18 ga watan Maris 2023 ƴan Najeriya za su fita domin kaɗa ƙuri'un su a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokoki na jihohi a faɗin ƙasar nan.
Sai dai zaɓen gwamnonin ba a kowane jihohi bane za a gudanar da shi ba. Wasu jihohin na Najeriya sam ba za su fita ba a wannan rana domin zaɓar gwamnonin su.
Za a gudanar da zaɓen gwamnan ne a jihohi 28 a faɗin ƙasar nan, yayin da ba za a yi zaɓe ba a cikin jihohi 8.
Dalilin da ya sanya ba za a gudanar da zaɓen gwamna ba a waɗannan jihohin shine ana gudanar da zaɓen sune a lokaci daban ba tare da sauran babban zaɓen gama gari ba.
Hakan ya faru ne saboda hukuncin kotu da ya taɓa soke zaɓen gwamnonin jihar a baya, ko kuma an taɓa tsige gwamnonin su a baya.
An Tafka Magudi: Dan Takarar Gwamnan PDP Yaki Yarda Da Kaddara, Zai Kalubalanci Sakamakon Zabe a Kotu
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit Hausa tayi duba kan jihohi 8 da ba za a gudanar da zaɓen gwamna ba a ranar Asabar mai zuwa.
1. Jihar Ekiti
An gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ekiti a watan Yunin 2022. Za a sake sabon zaɓen gwamna a jihar a shekarar 2026 lokacin da wa'adin gwamna Biodun Oyebanji, yake dab da zuwa ƙarshe.
2. Jihar Osun
A jihar Osun an gudanar da zaɓen gwamna a watan Yulin 2022. Jihar tana ɗaya daga cikin jihohi biyu da za ayi zaɓen gwamnoni a shekarar 2026.
3. Jihar Bayelsa
Zaɓen gwamnan jihar Bayelsa zai gudana ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.
A watan Nuwamban 2019 aka zaɓi David Lyon a matsayin gwamnan jihar, sai dai daga baya kotu ta soke zaɓen sa inda ta maye girbin sa da Duoye Diri. Hakan ya kawo tasgaro a kalandar zaɓen jihar.
Dubu Ta Cika: An Kama Mutane 79 da Suka Haddasa Rikici da Karya Doka Yayin Zaɓen Gwamna A Jihar Arewa
4. Jihar Edo
A ranar 19 ga watan Satumban 2020 aka gudanar da zaɓenm jihar Edo. Zaɓen gwamna na gaba zai gudana ne a watan Satumban 2024
5. Jihar Imo
Jihar Imo tana daga cikin jihohin da akayi babban zaɓen 2019 a cikin su, amma kotu ta ƙwace zaɓen a hannun Emeka Ihedioha, sannan ta ba Hope Uzodimna.
Uzodinma ya zama gwamna ne a shekarar 2020. Zaɓen gwamna na gaba a jihar zai gudana ne dab da ƙarewar wa'adin sa a shekarar 2023.
6. Jihar Kogi
Kamar jihohin Imo da Bayelsa, jihar Kogi zata zaɓi sabon gwamnan ta ne a cikin watan Nuwamban 2023.
Dukkanin jihohi ukun an yi zaɓen gwamna a cikin su ne a ranaku daban-daban da na babban zaɓen 2019.
7. Jihar Anambra
An gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021. Za a sake sabon zaɓen gwamnan jihar a watan Nuwamban 2025.
8. Jihar Ondo
Kamar jihar Edo, za ayi zaɓen gwamnan jihar Ondo a cikin shekarar 2024.
An gudanar da zaɓen gwamnan jihar ne a watan Oktoban 2020, shekara ɗaya bayan babban zaɓen 2019.
Asali: Legit.ng