Orji Uzor Kalu, Sani Musa Da Sauran Masu Neman Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa
Yayin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta yi nasarar lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dattawa a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, wasu yan majalisar da aka zaba karkashin inuwarta suna neman kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10.
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya fito ne daga yankin kudu maso yamma sannan mataimakinsa, Kashim Shettima ya fito daga arewa ta gabas.
Wannan ya sa ana ta kira ga cewar ya kamata a mika kujerar shugaban majalisar dattawa wacce ita ce ta uku ga yankin kudu maso gabashin kasar.
Sai dai kuma har yanzu jam'iyyar bata sanar da matsayinta ba a hukumance, hakan yasa kujerar ya zama a bude ga duk mai ra'ayi.
An tattaro cewa masu neman takarar kujerar na ta kamun kafa a wajen takwarorinsu gabannin rantsar da majalisa ta 10 a watan Yunin 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ga jerin manyan zababbun sanatoci biyar da ke da ra'ayi a kan kujerar.
- Barau Jibrin (APC daga Kano)
- Godswill Akpabio (APC daga Akwa Ibom)
- Orji Uzor Kalu (APC daga Abia)
- Sani Musa (APC daga Niger)
- Dave Umahi (APC daga Ebonyi).
Shugabancin majalisa ta 10: Ban tsayar da kowa ba, Inji Tinubu
A halin da ake ciki, zababben shugaban kasa Tinubu ya bayyana cewa bai tsayar da kowa don shugabancin majalisar dattawa ba.
Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu ya fadi hakan ne a taron kwamitin aiki na jam'iyyar APC mai mulki tare da zababbun mambobin majalisar dokokin tarayya da aka yi a fadar shugaban kasa, Abuja.
Zababben shugaban kasar ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima a taron.
Kungiyar Ohanaeze ta tsayar da Umahi domin zama shugaban majalisar dattawa
A wani labarin kuma, kungiyar dattawan kudu maso gabas, Ohanaeze Ndigbo sun lamuncewa Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi domin ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba.
Kamar yadda kungiyar ta bayyana, mikawa yankin wannan kujera ta uku a kasar zai tabbatar da adalci sannan zai sa su ga cewa ana yi da su sabanin zargin da suke yi na cewa an mayar da su saniyar ware a kasar.
Kungiyar ta yi kiran ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng