Jigon PDP Ya Yi Kira da Babbar Murya, Ya Fadawa Tinubu Bukatar Yarbawa a Mulkinsa

Jigon PDP Ya Yi Kira da Babbar Murya, Ya Fadawa Tinubu Bukatar Yarbawa a Mulkinsa

  • Ayodele Peter Fayose ya na so Asiwaju Bola Tinubu ya hada kan daukacin Yarbawan Najeriya
  • Tun da Yarbawa sun samu mulki, Tsohon gwamnan Ekiti yana so yankin Kudu maso yamma ya cigaba
  • Fayose ya bada shawara Tinubu ya rika dauko Yarbawa ‘yan adawa wajen raba mukaman gwamnati

Oyo - Tsohon gwamna a jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya ba Asiwaju Bola Tinubu shawarar ya yi tafiya da ‘yan adawarsa idan ya kafa gwamnati.

Ayodele Peter Fayose ya shiga gidan rediyon Fresh FM 105.9 da ke garin Ibadan a jihar Oyo, ya tattauna a game da abin da suka shafi siyasar Najeriya.

Da aka bukaci ‘dan siyasar ya ba Bola Tinubu shawarar inda zai kamo a mulki, sai ya bukaci ya rungumi kowa kuma ya hada-kan daukacin Yarabawa.

Ayo Fayose ya ce ba zai ba ‘dan siyasar wata shawara ba, amma yana so gwamnatinsa ta tafi da Yarbawa ba tare da duba sabanin siyasa ba.

Kara karanta wannan

Mukarrabin Jonathan Ya Fadi Yaudarar da Tinubu ya yi Amfani da Ita Wajen Doke Atiku

Ba sai an ba Tinubu shawara ba

A cewar tsohon Gwamnan, zababben shugaban kasar ya dade yana harin zama shugaban Najeriya, don haka ba zai rasa tsare-tsaren da ya tanada ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A matsayinsa na Jagoran Yarbawa, The Nation ta rahoto Fayose yana cewa shugaban kasar mai jiran gado yana bukatar ya hada kan ‘yan kabilarsa.

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu da Muhammadu Buhari a Daura Hoto: @ ABATMediaCentre
Asali: Twitter

Fayose ya ce zai yi kyau Yarbawa su rika yin magana da murya guda saboda cigaban yankinsu.

Jigon na PDP ya kuma nemi tsohon Gwamnan na Legas ya nada wata tawaga mai dauke da ‘yan jam’iyyar adawa da za su kawo manufofin cigaban kasa.

Shugaban kowa ba na 'Yan APC ba

A maimakon ya zama shugaban ‘Yan APC a Kudu maso yamma, Fayose wanda ya mulki Ekiti sau biyu yana so Tinubu ya zama shugaban duka Yarabawa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

Idan aka tashi rabon mukamai, ‘dan adawan ya ce ayi la’akari da duk wani Bayarabe ba sai ‘ya ‘yan APC ba, ya ce idan ya ji kunya, Yarbawa sun kunyata.

Kafin yanzu wasu Yarbawa sun fusata su na neman kasar kansu, rahoton ya ce Fayose yana ganin an kawo karshen koken nan tun da za su yi mulki.

'An kai LP an baro ta' - Reno

Rahoto ya zo da aka fahimci cewa Bola Tinubu ya yi amfani da abokan kasuwanci ne ya yaudari Peter Obi ya yi takara saboda a karya jam’iyyar PDP.

Reno Omokri yake cewa zababben Shugaban kasar ya nuna kwarewarsa wajen wasa da hankalin ‘Yan Obidient a 2023, suka dauka za su iya lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng