Sakataren PDP Na Jihar Ondo Ya Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Yi Martani Mai Zafi

Sakataren PDP Na Jihar Ondo Ya Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Yi Martani Mai Zafi

  • Sakataren jam'iyyar PDP da wasu jiga-jigai sun fice daga cikin jam'iyyar a jihar Ondo da ke arewa maso yamma
  • Mai magana da yawun PDP na jihar, Mr Kennedy Peretei, ya ce wannan ci gaban ba zai hana jam'iyyar rawar gaban hantsi ba
  • Ya ce ya kamata a raɗa wa irin waɗan nan mutanen suna karuwan siyasa kuma PDP tana masu fatan Alheri

Ondo - Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Ondo ta caccaki tsohon Sakatarenta da wasu jiga-jigai, waɗanda suka ɗauki matakin ficewa daga inuwar jam'iyyar.

Jaridar Punch ta tattaro jam'iyyar PDP na cewa matakin sauya shekar da suka ɗauka bai girgiza jam'iyyar ba.

Tutar PDP.
Tambarin jam'iyyar PDP Hoto: PDPNigeria
Asali: Twitter

A wata sanarwa da kakakin PDP, Mr Kennedy Peretei, ya fitar, ya ce shugabancin jam'iyya ya samu rahoton cewa Okunomo ya yi murabus, amma hakan ba zai hana su bacci ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kashe Kansila Mai Ci, Sun Banka Masa Wuta a Jihar APC

Sanarwan ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A watanni 18 da suka shige, masu irin wannan halayyar sun shigo kuma sun fita daga PDP har sau biyu, hakan alama ce da ke nuna su yan siyasa ne da basu iya zama wuri ɗaya."
"Mafi yawa PDP ta ɗaukaka su fiye da matsayinsu, sun sha kaye hannun wasu jam'iyyun siyasa a mazabunsu lokacin zaben da ya gabata. A ko da yaushe rashin nasara ke bin son ransu da burin da suka sa a gaba."
"Da farko sun koma Zenith Labour Party amma marasa kunyan suka sake dawowa PDP bayan gaza samun abinda ransu yake so."

Kakakin PDP ya ƙara da nuna mamakin me zai hana jam'iyya bacci kan abinda ya kira mara amfani, mashahuran masu sauya sheka.

Mista Peretei ya ce ba zai yi mamaki ba idan aka raɗa wa irin waɗan nan mutanen sunan karuwan siyasa duk inda suka je.

Kara karanta wannan

Babban Jigo Kuma Tsohon Gwamna Ya Bar Inuwar Atiku Zuwa APC? Gaskiya Ta Bayyana

Daga karshe ya ce PDP na musu fatan alkairi, kuma, "Duk lokacin da suka zabi dawowa kofa a buɗe take. Yanzu dai sun nuna su makiyaya ne a siyasa."

Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Lashe Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas

A.wani labarin kuma Gwamna Okowa na Delta ya bayyana abubuwan da suka baiwa Peter Obi nasara a shiyyoyi guda biyu.

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP ya ce Obi ya yi amfani da addini, Obidient da wasu dabaru wajen nasara a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262