Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar NNPP Ta Juyawa Ɗan Takarar Gwamnanta Na Katsina Baya
- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Katsina, ta marawa ɗan takarar gwamnan APC, Dikko Radda, baya
- An samo cewa shugabannin jam'iyyar sun juyawa ɗan takarar gwamnan ta, Nura Khalil, baya kan cewa ba zai iya cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe ba
- A cewar shugaban jam'iyyar NNPP na jihar, Alhaji Sani Liti, gabaɗaya shugabannin jam'iyyar suka yanke shawarar su marawa Radda baya
Jihar Katsina- Shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihar Katsina, Alhaji Sani Liti, ya bayyana dalilin da ya sanya wasu mambobin jam'iyyar suka marawa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC, Dikko Umar Radda, baya a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.
Liti, a wata ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, yace shugabannin jam'iyyar sun zaɓi Radda ne saboda basu da ƙwarin guiwa akan ɗan takarar su, Engr Nura Khalil. Rahoton PM News
Shugaban jam'iyyar ya kare hukuncin da suka yanke na marawa ɗan takarar jam'iyyar APC, baya, inda ya ƙara da cewa shugabannin jam'iyyar na jihar Katsina sune suka yanke wannan hukuncin.
Da yake kare goyawa Dikko Radda, baya, Liti, yayi iƙirarin cewa rashin ƙwarewar Nura Khalil, shine abinda ya tilasta gabaɗaya shugabannin jam'iyyar komawa bayan ɗan takarar APC, wanda suka yi amanna cewa zai yi abin arziƙi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga cikin manyan jiga-jigan shugabannin jam'iyyar NNPP ta jihar da suka marawa Dikko Radda, baya akwai, sakataren jam'iyyar, Alhaji Umar Jibril, shugaban matasa, Mustapha Basheer.
Sauran sun haɗa da, shugaban jam'iyyar na shiyyar Katsina, Dauda Kurfi, shugaban jam'iyyar na shiyyar Funtua, Abdulhadi Mai-Dawa, shugaban jam'iyyar na shiyyar Daura, Sale Mashi da Sanata Audu Yandoma.
Legit Hausa ta samu zantawa da wani ɗan jam'iyyar NNPP a jihar Katsina, Mubarak Nalami, wanda ya nuna rashin jindaɗin sa kan wannan goyon baya da shugabannin jam'iyyar suka yiwa ɗan takarar APC.
"Ban jidaɗin wannan abin da shugabannin jam'iyyar mu suka yi mana ba ko kaɗan. Hakan ba ƙaramar matsala zai janyowa ɗan takarar gwamnan mu ba."
Ya nuna rashin ƙwarin guiwar sa kan samun nasarar ɗan takarar jam'iyyar ta su a dalilin wannan juya masa baya da shugabannin suka yi masa.
"A maganar gaskiya da wuya ɗan takarar mu ya kai labari a zaɓen gwamnan dake tafe, saboda wannan abin da shugabannin jam'iyyar suka yi ba ƙaramin naƙasu zai kawo masa ba. Amma ba komai su je sun yiwa kan su."
Zaɓen 2023: Peter Obi Ya Bayyana Takamaiman Abinda Ya Sanya Ya Garzaya Kotu
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, ya bayyana dalilin sa na garzayawa kotu kan zaɓen Tinubu.
Peter Obi ya bayyana takamaiman dalilin da ya sanya ya tafi kotu bayan hukumar INEC ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Asali: Legit.ng