Kudu Maso Gabas Na Iya Samun Shugaban Majalisar Dattawa Yayin da Tinubu Ke shirin Kafa Gwamnatin Hadin Kai
Duk da koken da ake yi dangane da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na ta shirye-shiryen kafa gwamnatinsa gabannin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Maris.
Wani rahoton Vanguard ya bayyana cewa Tinubu zai gana da zababbun yan majalisar dokokin tarayya a ranar Litinin, 13 ga watan Maris a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
An tattaro cewa babban ajandar taron zai ta'allaka ne kan yadda za a raba manyan mukamai na majalisun dokokin tarayya.
Kudu maso gabas za ta samu shugaban majalisar dattawa
Majiyoyi da Vanguard ta ambata sun ce Tinubu yana shirin kafa gwamnati ta hadin kan kasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Saboda haka, an ce zabbaben shugaban kasar ya yarda ya mika shugabancin majalisar dattawa ga yankin kudu maso gabas domin magance matsalar mayar da su saniyar ware.
An tattaro cewa Sanata Orji Uzor Kalu ne mafi soyuwa don zama shugaban majalisar dattawa na gaba idan aka mika kujerar kudu maso gabas.
Gbajabiamila shugaban ma'aikata
Hakazalika, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila na iya zama shugaban ma'aikatan shugaban kasa na gaba.
Koda dai ya lashe zabensa na komawa majalisar wakilai, ana ta rade-radin cewa Gbajabiamila na da ra'ayi kan matsayin.
An tattaro cewa Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, shima yana iya hawa matsayin amma watakila a bashi wani matsayin a gwamnatin Tinubu.
El-Rufai ko Ganduje wani na iya zama babban sakataren gwamnatin tarayya
A halin da ake ciki, majiyoyin da Vanguard ta ambata sun ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Abdullahi Ganduje na jihar Kano sune ake duba yiwuwar ba mukamin sakataren gwamnatin tarayya.
Sauya kudi: Rashin bin umurnin kotun koli na iya haifar da rikici, ACF
A wani labari na daban, zauren tuntaba ta arewa wato ACF ta ja hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan hatsarin da ke tattare da kin bin umurnin kotun koli game da sauya fasalin kudi.
A cewar kungiyar ta arewa, wannan manufa ta CBN ka iya haifar da tashin hankali a fadin kasar idan har aka ci gaba da kin aiwatar da hukuncin kotun koli na ci gaba da amfani da tsoffin kudi.
Asali: Legit.ng